Manyan yan Arewa ba za'a manta da su ba

Manyan yan Arewa ba za'a manta da su ba

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan Arewa wanda ya hau karagar mulkin kasar Najeriya a ranar Juma'a, 29 ga watan Mayun Bara

- Da iznin Ubangiji, kasar Najeriya zata yi bikin yancin kai na 56 a ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba, 2016

- Akwai manyan yan Arewa daban daban wadanda sunyi abubuwa ba zamu manta da su ba a lokaci kasar Najeriya ta dauki yanci kai daga kasar Biritaniya a shekarar 1960

Ku duba sunayen da hotunan wasu yan Arewan a kasa:

1. Sir Ahmadu Bello (Sardauna na Sokoto)

Shine Firamiya na yankin Arewacin kasar daga 1954 zuwa 1966. Dan asalin Sakkwato ne. Idan yake so matsayin Firaym Minista kafin yancin kai a 1960, yakamata ya dauki ta. Amma, bai yi ba.

Manyan yan Arewa ba za'a manta da su ba
Ahmadu Bello

Shugaban Arewacin kasar da wani Jarumi wanda yan Arewa ba zasu manta da shi ba har abada. An kashe shi a juyin mulkin soja a watan Janairu, 1966.

2. Sir Abubakar Tafawa Balewa (Firaym Minista daga 1959 zuwa 1966)

Dan asalin jihar Bauchi ne. Yayi aikin Malamin makaranta kafin ya zama Firaym Minista. Yana tsakanin daliban siyasar Ahmadu Bello. Ba abun kamar soyayyan kudi ko sha'awan duniya acikin zuciyarsa. Mai hakuri, mai gaskiya ne. Ba ruwansa da dukiya ko arziki.

Manyan yan Arewa ba za'a manta da su ba
Abubakar Tafawa Balewa

An bashi sunan 'Golden Voice of Africa,' domin yana da murya mai kyau. Kuma, an kashe Tafawa Balewa a juyin mulki na farko a kasar a watan Janairun 1966. Babban Jarumi ne.

3. Isa Kaita, ministan ilmi a shekarar 1959

Manyan yan Arewa ba za'a manta da su ba
Isa Kaita, Wazirin Katsina

KU KARANTA KUMA: Hauhawan tattalin arziki ya fara saukowa

4. Aliyu, Makaman Bida, ministan kudi a 1959

Manyan yan Arewa ba za'a manta da su ba
Aliyu Makama Bida

5. Shettima Ali Monguno, ministan Mai

Manyan yan Arewa ba za'a manta da su ba
Shettima Ali Monguno

6. Michael Buba, ministan zaman takewa jin dadin a 1959

Wanna minista, sunansa gaba daya ne Michael Audu Buba. Dan siyasar Najeriya da sunan Wazirin Shendam. Yana tsakanin yan majalisa a majalisar dokokin Arewacin kasar.

Manyan yan Arewa ba za'a manta da su ba
Michael Buba

KU KARANTA KUMA: Wasu 'yan siyasa da su ka yi kaurin suna

7. Maitama Sule, Danmasanin Kano

Manyan yan Arewa ba za'a manta da su ba
Maitama Sule

Kuma akwai Ibrahim Musa Gashash, ministan asashe da kuma bincike a 1959; akwai Usman Galadiman Maska, ministan harkokin ciki; akwai Abba Habib, ministan kasuwa a 1959; akwai Maikano Dutse, ministan kananan hukumomi a 1959 da kuma akwai Abdullahi Jada 1959 ministan lafiyar dabbobi a 1959.

Sun duk, sunyi kokari sosai dasu kawo cigaba zuwa ga yankin Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel