Abubuwa 5 game da Akeredolu

Abubuwa 5 game da Akeredolu

Rotimi Akeredolu, a karshen satin nan ya samu nasarar zama dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ondo da za'a yi ranar 26 ga Nuwamba 2016.

An bashi nasarar lashe zaben fidda gwani da akayi na jihar Ondo ranar Assabar, 3 ga Satumba a cikin matakan tsaro a babban birnin jihar dake Akure.

Akeredolu, ya doke Dr Segun Abraham  na hannun damar jigon jam'iyyar na kasa wanda ya samu kuri'u 635 yayin da Chief Olusola Oke yazo na ukku da kuri'u 583. Sanata Ajayi Boroffice yazo na hudu da kuri'u 471

Abubuwa 5 game da Akeredolu
Chief Rotimi Akeredolu (SAN)

Ga abubuwan da ke da ban sha'awa game da Mr Akeredolu:

1.Lokacin daya shugabanci NBA

Tsohon shugaban kungiyar lawyoyin Najeriya ne (NBA). Ya zama shugaban kungiyar a 2008. A Nuwamba 2009 aka zarge shi da cin rashawa. Mataimakin shugaba, sakataren walwala da mukaddashin sakataren kudi sun rubuta takardar koke mai suna "Koke-koke game da kai kan damfara da karya kaidojin NBA". Daga karshe, hukumar zarraswa ta kungiyar tayi watsi da zarge-zargen

2. Iyali

An haifi Akeredolu cikin iyali masu addini, mahaifinsa Reverend J. Ola Akeredolu, kuma mahaifiyarsa mai wa'azi ce koko Lady Evangelist Grace B. Akeredolu  daga iyalin Aderoyiju daga Igbotu, Ese Odo ta jihar Ondo. Yayin da yake girma ya dauki hanyarsa dabam inda ya halarci jami'ar Ife wadda ake kira jami'ar Obafemi Awolowo yanzu inda ya karanta harkokin shari'a ya kuma sauka a shekara ta 1977, ya kuma zama cikakken lawya a 1978.

KU KARANTA:Tinubu ya gana da Aregbesola kan dan takarar zaben Ondo

3. Shigarshi siyasa

Ba bako bane a siyasa, domin yayi takarar gwamnan jihar a 2012 karkashin tsofuwar jam'iyyyar Action Congress of Nigeria (ACN). Ya kara da gwamna mai ci Olusegun Mimiko da Mr Olusola Oke na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Akeredolu yayi alkawarin samo ayyuka 30,000 a cikin kwanaki 100 in yaci nasara, abinda dan takarar PDP ya kira dabo

4.Mutunci

Abin mamaki, a shekara ta 2012, kungiyar lawyoyin ta sama sabusar  sakatariyarta sunansa tana bada dalilin yin haka da cewa akwai bukatar " fiddo wadanda suka sa kungiyar ta fifita, da kuma ci gaban kungiyar"

5.Karatunsa

Ana girmama  Akeredolu cikin masana. Ya halarci makarantar Loyola college a Ibadan, kuma shine babban lawyan gwamnatin jihar Ondo tsakanin 1997–1999. Ya zama babban lawyer watau Senior Advocate of Nigeria (SAN) 1998. Bayan ya fadi zaben 2012 ga Olusegun Mimiko, ya dawo da zama cikin jihar Ondo domin kasancewa kusa da jama'a da kuma sa ido ga gwamnatin Olusegun Mimiko.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel