Karon batta tsakanin dan ‘union’ da sojan ruwa

Karon batta tsakanin dan ‘union’ da sojan ruwa

Wani jami’in kungiyar direbobi ta NURTW ya sha mari hannun wani sojan ruwa a saboda ya yi masa taurin kai

A cewar wani wanda abin ya faru a indonsa, ya ce al’amarin ya faru ne a jihar Lagos a yayin da dan yuniyon din ya yi kokarin karbar kudin ka’ida a wurin direban motar da sojan ya ke ciki.

Karon batta tsakanin dan ‘union’ da sojan ruwa
Sojojin Ruwa a yayin wani atisaye

Shi kuma direban motar hayar ya yi kememe, a bisa dalilin cewa yana dauke da yallabai mai kayan sarki, shi kuwa dan uniyon ya dage sai ya karbi kudin na ka’ida.Wannan, a cewar wanda lamarin ya faru a gabansa, ta sa sojan ya sa baki a takaddamar a tsanake, amma kuma, a cewar majiyar, ya harzuka dan uniyon.

KU KARANTA: Abubuwan Tir da wasu coci-coci suka aikata a Nigeria

Kan kace 'kwabo' yallabai sojan ruwa ya sauko ya kuma kawashe dan yuniyon da mari zafafa wadanda suka sa shi ganin taurari da tsakar rana a kuma gaban taron jama’a. Ana haka ne, a cewar majiyar, sai ga wata motar sintiri ta sojin wacce ta iso wurin kamar an jefota, a inda ta yi awon gaba da sojan ruwa mai yin mari.

KU KARANTA: Burin CJTF 250 a Borno ya cika

Irin wannan arangama tsakanin jami’an soja ba sabon abu ba ne a jihar, domin a kwanakin baya a jihar wani sojan kasa ya yiwa wani kwandasta jina-jina a wurin shiga mota, haka kuma wasu fusatattun ‘yan jihar suka yiwa wasu jami’an kiyaye hadari dukan-kawo-wuka a bisa zargin cewa sun haddasa hadarin wata mota a inda mutane uku suka mutu, a wata mahadar da jami'an ke bayar da hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel