Kocin Super Eagles na Najeriya 5 da suka bar tarihi

Kocin Super Eagles na Najeriya 5 da suka bar tarihi

Kocin Super Eagles na Najeriya 5 da suka bar tarihi.

Kocin Super Eagles na Najeriya 5 da suka bar tarihi

 

 

 

 

 

 

Yayin da Hukumar NFF ta ke kokarin hayar farin fata a matsayin Darektan wasanni da na Super Eagles da cewa hakan kadai ne zai kawo karshen matsalar da Kungiyar kwallon ke fuskanta, mun kawo maku jerin Kocin Kasar wadanda suka yi namijin kokari, har suka kafa tuta, suka yi zarra cikin wadanda suka taba horar da Super Eagles na Najeriya. Ga biyar (5) nan daga cikin su:

1. Clemens Westerhof:

An nada Westerhof Kocin Super Eagles na Kasar a shekarar 1989, Ya kai Kasar Gasar AFCON 90 inda Najeriya ta zo ta biyu a Gasar na zakarun Nahiyar Afrika. Westerehof ne Kocin da ya jagoranci Kasar ta kuma ci kyautar azurfa a Gasar ta AFCON 92 da aka buga a Senegal, Super Eagles ne suka zo na 3. Koci Westerhof bai tsaya nan ba, A shekarar 94 Najeriya ta daga Kofin AFCON a Kasar Tunisiya, Westerhof ya jagoranci Kasar Najeriya zuwa Gasar cin kofin duniya watau World Cup na 1994 da aka buga a Kasar Amerika, sai dai Kasar Italiya ta yi waje da Najeriya a zagaye na biyu. Bayan nan ya samu matsala da mutanen na sa, ya bar aikin na Super Eagles

2.  Bonfrere Jo:

Ko kana jin Atlanta 96, wannan Kocin ne ya ciwo ma Najeriya kofin Olympics na masu kasa da shekaru 23, Najeriya ce Kasar da ta zo na daya, aka bata kyautar gwal a Gasar Olympics da aka buga a Birnin Atlanta a shekarar 1996, abin da ba a taba samun wata Kasar Afrika tayi ba a baya. Yayi aiki daga baya a matsayin Darektan wasanni na Kungiyar Super Eagles har ya kai Kasar wasan karshe na Gasar AFCON, sai dai Kasar Kamaru tayi nasara a bugun finariti.

3.   Shuaibu Amodu:

Marigayi Amodu mutumin Kasar Edo ne, shine Kocin gidan da ya fara kai Najeriya Gasar World Cup a shekarar 2002 da kuma 2010. Amodu ya jagoranci Najeriya ta zo na uku a Gasar AFCON da aka buga shekarar 2002 da 2010 a lokacin sa. Amodu dai yana cin Kocin da ba a ganin kimar su, amma shakka babu, yana cikin gwanayen Kocin Super Eagles da mu ka taba samu a tarihim Kasar nan.

4.  Stephen Keshi:

Cikin dan kankanin lokaci, Stephen Keshi ya bar tarihi a Najeriya da ma Afrika. Cikin shekaru uku rak, Marigayi Keshi ya ci ma Najeriya Kofin AFCON na Afrika shekarar 2013, ya kuma jagoranci Super Eagles na Kasar zuwa Gasar Confederations Cup a Kasar Brazil. Marigayi Keshi ya jagoranci Super Eagles zuwa zagaye na biyu a Gasar World Cup 2014. Shine na biyu a duniya da ya taba cin kofin AFCON yana dan kwallo, kuma ya dawo ya ci a matsayin Koci da Super Eagles.

5.   Samson Siasia:

Samson Siasia ya kafa tuta wajen aikin U-20 da kuma U-23 na Kasar. Ya je daf da cin Kofin U-20 da aka buga a Kasar Nederlands, ya kuma jagoranci Flying Eagles na Kasar a Shekarar 2008, inda ya rasa Kofin ga Kasar dai ta Argentina, Siasia yayi kaurin suna a Gasar Olympics na Beijing, inda mutumin Bayelsan na Najeriyar ya tafi da yan wasa 14 rak, kuma har ya samu kyautar azurfa. Yanzu haka ana kuma shirin buga wani Gasar na Olympics a Garin Rio inda Siasia ya kudiri niyya. Ya taba horar da Super Eagles na Kasar.

KU KARANTA: Samson Siasia ya kafa tuta wajen aikin U-20

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel