Sayayya 10 mafi tsada a tarihin kwallon kafa a duniya

Sayayya 10 mafi tsada a tarihin kwallon kafa a duniya

LABARIN WASANNI

Sayayya 10 mafi tsada a tarihin kwallon kafa a duniya

 

 

 

 

 

Yayin da duniya ke jiran a tabbatar da cinikin Paul Pogba wanda zai kama kusan fam miliyan £100 daga Juventus zuwa Man Utd, idan hakan ta tabbata, to zai zama sayayyan da ya fi kowane tsada a duniya. Legit.ng ta kawo maku sauran sayayyen da su ka fi kowane tsada a duniya. Ban da shahararru irin su Cristiano Ronaldo da Bale da aka sani, akwai wasu hala wadanda ba a sani ba. Ga dai jerin ‘yan wasa 10 nan, wadanda cinikin su ya fi na kowa tsada a duniya.

Kungiyar Man City, wanda tayi kaurin suna wajen barnar kudi ta sayo sa wancan shekarar a kan makudan kudi har fam miliyan £55 daga Wolfsburg. Dan wasan na tsakiya ainihin dan Kasar Belgium ne.

Dan wasan duniya na Shekarar 2007, Ricardo Kaka ya bar AC Milan ta Italiya zuwa Real Madrid shekarar 2009 kan kudi fam miliyan £56.

A ranar da aka sayi dan wasa Zlatan, an saida rigunan sa sama da 80,000. Dan wasan na Kasar Sweden ya shiga tarihi ne lokacin da Barcelona ta sayo sa daga Inter Milan kan kudi fam miliyan £56 a shekarar 2009. A cinikin Barcelona ta hada da dan wasan ta Samuel Eto’.

Cinikin Di Maria ne wanda ya fi kowane tsada a Kasar Birtaniya. Man Utd ta bada kudi har fam miliyan £59.7 ga Real Madrid a shekarar 2014. Sai dai bayan shekara daya rak, dan wasan ya kara gaba.

Bayan dan wasa James ya nuna kan sa a World Cup, tuni Kungiyar Real Madrid ta sayo dan wasan na Kasar Colombia kan kudi miliyan £63 daga Kungiyar Monaco.

Tauraron Kasar Brazil, Neymar ya ci ma Bareclona akalla fam miliyan £71.5, an sayo sa ne daga Kungiyar Santos da ke Brazil bayan an dauki dogon lokaci ana ta rade-radi.

Ba za a manta da Suarez ba ko dan gartsawa jama’a cizon da ya saba. Haka Barcelona ta lale kudi har fam miliyan £75 ta saye dan wasan na Kasar Uruguay daga Liverpool.

Tsohon dan wasan gaba na Kungiyar Real Madrid Higuain, ya koma Juventus da Kungiyar Napoli kwanaki kadan da suka wuce kan kudi miliyan £75.3. Higuain ya karya wani tarihi da aka kafa tun shekaru 66 da suka wuce baya.

Dan wasan da ya fi kowa tsada a duniya kenan kafin shekarar 2013, Man Utd ta saida Ronaldo zuwa Real Madrid kan kudin da ba a taba ganin irin su ba a wancan lokaci, fa miliyan £83.7 a shekarar 2009. Yanzu dai haka kaf tarihin kulob din na Real Madrid babu wanda ya taba cin kwallaye kamar Cristiano, kuma yana kan ci har gobe.

Dan wasa Bale na Kasar Wales shine dan wasan da ya fi kowa tsada a duniya. Kungiyar Real Madrid ta kashe fam miliyan £93.1 wajen sayen dan wasan daga Tottenham shekaru uku da suka wuce. Kawo yanzu, Bale yaci kofin Uefa Champions League biyu a zaman san a Real Madrid.

KU KARANTA: INA AKA KWANA WAJEN BATUN KOMAWAR POGBA MANU UTD?

Asali: Legit.ng

Online view pixel