Fastocin Kasar nan sun yi addu’a ga Shugabannin banza

Fastocin Kasar nan sun yi addu’a ga Shugabannin banza

 

– Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo da Iyalin sa, haka kuma Shugaban Majalisar Wakilai, Dogara Yakubu na daga cikin wadanda suka hallarci wannan taro.

– An yi addu’a ga tattalin arzikin Kasar, Darajar Naira, Matasa, sauran mutane‘Yan Kasa, Harkar ilmi da kuma sauran matsalolin da ake fuskanta.

– Fasto Paul Adefarasin ne ya jagoranci addu’ar da aka yi ma Kasar game da tattalin arzikin, yace tattalin arzikin Najeriya na a daure.

Fastocin Kasar nan sun yi addu’a ga Shugabannin banza

 

 

 

 

Manyan limaman addinin Kirista na Najeriya sun yi addu’a ga Shugabannin Kasar. Wasu daga cikin Fastocin Kasar sun roki Ubangiji da ya kori duk Shugabbanin banza daga kan kujerar su. Limaman na Kirista sun taru ne a babban filin wasan Kasar da ke Abuja, suna rokon Ubangiji da ya kawo ma Kasar ta Najeriya daukin halin da aka shiga. Jaridar Vanguard ta rahoto wannan labari, tana mai cewa Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ce ta shirya wannan taron addu’a da aka ma suna ‘Nigeria Prays’. Mataimakin Shugaban Kasar, Yemi Osinbajo tare da iyalin sa sun halarci wannan taro. Haka kuma Shugaban Majalisar Wakilai na Kasar, Yakubu Dogara na cikin sauran manyan jami’an Gwamnati da suka samu halartar wannan taro na addu’a.

KU KARANTA: GWAMNA AYO FAYOSE YACE SHI WANI KARAMIN UBANGIJI NE

Manyan limaman Kiristan da suka yi addu’a dun hada da: Fasto Enoch Adeboye (Daga Cocin Redeemed Christian Church of God), Bishof David Oyedepo (Na Cocin David Oyedepo), Fasto William Kumuyi (Babban Limamin Deeper Life Church), Mataimakin Shugaban Kungiyar CAN ta Kiristocin Kasa, Farfesa Joseph Otubu. Saura dai sun hada da; Nicholas Okoh, Wale Oke, Dr DK Olukoya. Manyan jami’an Gwamnatin Kasar sun hallarci taron ko kuma dai sun tura wakili daga fadin Tarayyar Kasar. An dai yi addu’o’in ne kan matsalolin da suka shafi Kasar, hada da; Matsalar tattalin arziki, rashin aikin yi ga matasa da sauran su.

Fastocin sun yi addu’a ga Ubangiji da ya tunbuke duk wani Shugaba a Kasar wanda ba ya son talakawa. Haka kuma Fasto Dr Samuel Chukwuemeka Kanu Uche, yayi addua cewa duk Gwamnan da ba ya aiki, kar ya samu karasa wa’adin sa.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel