Abu 7 da zaka sani kafin auren kabilar Yoruba

Abu 7 da zaka sani kafin auren kabilar Yoruba

Yan mata kabilar Yoruba kamar sauran matan kabilu ne da suka iya zaman aure da kwarkwasa irin na aure. Da yawan su kuma su kan dade basuyi aure ba don haka sukan samu wayewar rayuwa sosai kafin auren. Hakan yakan sa su iya kula da gida sosai.

Abu 7 da zaka sani kafin auren kabilar Yoruba

A cikin wannan makalar, zamu bayyana ma mai karatu ne abubuwa 7 da yakamata ya sani kafin ya auri mata yar kabilar Yoruba. Aure wani babban sha'ani ne ganin cewa mutane ne biyu mabanbanta da ke zama a wuri daye tare kuma da begen su ida rayuwar su a tare har abada.

1. Ranar Asabar mai cike da shagali: kafin ka auri mata kabilar Yoruba, ya kama ta kasan cewa su fa duk ranar Asabar ta karshen mako suna da shagali ko ma shagulgulan da za su je. Wani lokacin ma ko ba'a gayyace su ba za su samu wanda zasu je.

Yarbawa mutane ne masu son shagali da bidio'i.

Wannan kuma yana nuna cewa dole ne mijin ta ya shirya ma siyen kayan anko a ko da yaushe.

2. Sai ka gaji da gaisuwa: Kowa yasan yadda yarbawa suke da ladabi da biyayya. To suna da gaisuwa sosai. Zasu gaida da ka da ka tashi bacci sannan haka kuma idan zaka fita aiki. Idan ka dawo ma zaka sha gaisuwa haka zalika idan zaka kwanta ma. Kai! In takaice maka labari koma yaushe ne zaka samu akwai kalar gaisuwar da zata yi maka.

3. Dole ne ka rika tsawatawa game da tsafta: dole ne ka zama mai kyama da kyankyami in dai kana so ka zauna lafiya da ita. Dole ne ka zama mai tsawatawa ga reta game da tsafta.

Sanannen abu ne cewa yarbawa ba su da tsafta can-can.

4. Akwai son girki: mata kabilar yarbawa akwai son girki. Dafa abinci bai bata masu rai ko kadan. Zaka samu cikakkiyar macen kabilar yoruba bata damu ba ta tashi da sassafe ta dafa abinci, haka ma da rana kai harma da dare.

Tabbas zaka ci ka koshi idan ka auri bayarba don bazata taba barin ka da yunwa ba.

5. Akwai mallake miji: Matan yarbawa akwai mallake miji. Idan ma kasan wasa kakeyi to kar ka kuskura ka matsi matan yarbawa don kuma su da gaske za su dauki abun kuma za su iya bin duk hanyar da za su iya son suga sun mallake ka. Zasu iya yadda su yi ciki kuma suki subda shi sabo dai dole ka dawo musu.

6. Sun iya kwalliya: matan yarbawa akwai iya caba kwalliya. Amma ba muna nufin duka ba, a'a akwai yan gayun su sosai kuma yan gayun nasu sun iya kwalliya sosai.

7. Akwai shan yaji: Indai har kana son zama da mata kabilar yoruba to kam dole ne ka koyi shan yaji. Akwai su akwai shan yaji sosai. Kusan duk abincin su sai sun sa shi ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel