Ifeanyi Uba sun saya sabbin yan wasa guda uku

Ifeanyi Uba sun saya sabbin yan wasa guda uku

Kungiyar kwallon kafa ta Ifeanyi uba dake buga gasar Najeriya firimiya leg sun saya yan wasa guda uku domin su taimaka ma kungiyan dan ta samu daman tsayawa da kyau a gasar zakarun najeriya wato (NPFL) a shekarar 2015/2016.

Ifeanyi Uba sun saya sabbin yan wasa guda uku
sabbin yan kwallon Emmanuel Okoh, Ejiogu Chijioke and Adah Stephen

Yan wasan garin Anambura sune na 11 a teburin gasar NPFL a inda wasan su na gaba zasu hadu da kungiyar kwallon kafa ta sunshine stars dake garin Akure a Nnewi. Yan wasan da suka saya, sun hada da Emamanuel Okoh wanda yazo daga Mighty Jets. Sai mai tsaron ragar Enyimba mai suna, Ejiogu Chijioke shima zai hadu da Ikechukwu Ezenwa a kungiyar. Haka kuma danwasa mai suna Adah Stephen wanda ke buga ma sunshine sters gaba shima ya ajiye ya Akuren a gefe inda ya garzaya kungiyar ta ifeanyi uba.

A lokacin da yake magana da Legit.ng sports, mai magana da yawun yan kungiyar, Diegwu Nwankwo ya bayyana cewar dalilin sayan yan wasan saboda su taimaka ma yan wasan da kuma kungiyar tacigaba.

Ya kara dacewa, muna bukatar mu kara yawan ya wasa masu hazaka a kungiyar mu. Wannan shi zaisa yan wasan kowa yayi kokarin samun waje a filin wasa, kuma a tunanina, gasar bai kare ba har yanzu, domin kuwa muna so muyi wasa da yan waje a shekara mai zuwa ina ganin hakan cigaba ne mai yawan gaske.

Asali: Legit.ng

Online view pixel