Ba zamu yarda yan bindiga na hallaka mu ba – Yarbawa

Ba zamu yarda yan bindiga na hallaka mu ba – Yarbawa

-    Dattawan yan kabilan Yarbawa sun ce lallai fa, ba zai yiwu yan bindiga su dinga hallaka rayuwan mutanen yankin Kudu maso Yamma ba

-    Sun  rantse sai sun hukunta Makasan

-    Sun gargadin cewa ‘shiru shiru fa,ba tsoro bane

Dattawan yan kabilan Yoruba karkashin kungiyar hadin kan Yoruba watau ‘Yoruba Unity Forum(YUF)’sun yi ca da hare haren da yan bindigan Neja Delta ke kai wa mutanen yankin Kudu maso Yamma ya saba hankali kuma sai ya isa hakan.

An kwana biyu ‘yan bindiga da ake zargin yan yankin neja delta ne da suka shigo yankin legas ta ruwa, suna kai ma yan yankin hare-hare. Hari mafi kusa kusan da suka kai shine harin da aka kai unguwar ikorodu inda aka rasa rayuka 30 bayan yan bindigan sun bude musu wuta.

Kungiyar ta kai kukan ta’asan Fulani makiyaya,yan bindiga da yan garkuwa a yankin yarbawan.

A wata jawabin da Shugaban Kungiyar ,Emmanuel Gbonigi, da Sakataren ,Senata Anthony Adefuye, suka sanya hannu, dattawan sun ce wannan hare haren na tayar da hankalin da kasa gaba daya. Sun ce baza su zauna kara zube yankin Kudu maso Yamma ya zama filin dag aba kuma sun rantse sai yan bindigan sun amsa tambayoyin laifin su.

“Kasar Najeriya na cikin wani halin ha’ulahi na rashin tsaron rayuka da dukiya. Yankin Kudu maso Yamma da aka sani da zaman lafiya ma an fara kai mata hari kwanan nan,duk da ayyukan Fulani makiyaya a yankin.

Wadanan hare haren na zuwa daga wani makiyi da bamu taba fuskantar juna ba,yankin Neja Delta. Kisan gillan da wadannan mutanan suka yi ma mazauna Igbolomu da Ishawo cikin karamar Hukumar Ikorodu a Jihar Legas,sai su amsa.  Mutanen yankin Kudu maso Yamma masu zaman lafiya ne,masu hakuri ne,masu karrama baki ne,kuma salihan makwabta ne”.

KU KARANTA : Yan bindiga sun sha alwashin kai hari ga gwamnatin jihar Imo

Hakazalika, yan bindigan Neja Delta sun kai hari kauyen Jihar Ogun. Sun shiga unguwar Imushin, Ogijo na Jihar Ogun da daren 17 ga watan yuni, kuma sun hallaka rayuka akalla 15.

Asali: Legit.ng

Online view pixel