Messi ya kafa tarihi a gasar Copa America dake gudana

Messi ya kafa tarihi a gasar Copa America dake gudana

Shahararren dan kwallon nan Lionel Messi ya zamo dan kwallon da yafi kowa zura kwallo a kasar sa ta Argentina biyo bayan zurawar da yayi lokacin da kasar tasa ta doke kasar Amurika mai masaukin baki 4 - 0. Ita dai kasar Argentina din yanzu ta samu tikitin buga wasan karshe na gasar.

Messi ya kafa tarihi a gasar Copa America dake gudana
Messi

Shahararren dan wasan gaban na kulob din Barcelona ya zura kwallon ne daga bugun bango 'free kick' wanda hakan ne kuma ya bashi damar wuce Gabriel Batistuta wanda ya ciwa kasar tasa kwallo 54. Messi din dai shine ya fara taimaka wa Ezequiel Lavezzi wajen zura kwallon farko kafin shi da kansa ya jefa ta 2 sannan daga bisani Gonzalo Higuain ya jefa ta 3.

"Na ji dadi da na kafa wannan tarihin sannan kuma ina gode ma abokan kwallon nawa saboda da su ne kawai hakan ya tabbata kuma suma nasarar tasu ce" inji dan kwallon da zai cika shekaru 29 ranar Juma'a mai zuwa. Ita dai Argentina tuni ta samu tikitin buga wasan karshen inda zata buga shi da kasar Colombiya ko kuma masu rike da kambun watau kasar Chile. Za'a buga wasan ne ranar Laraba mai zuwa a garin Chicago.

Ku karanta: Ibrahimovic naso ya koma Manchester United

Wani cikin magoya bayan kasar tasu dai ma ya shigo cikin finin dab da a fara kashi na biyu na wasan inda yaje wurin Messi ya durkusa masa. Mai karatu zai iya tunawa cewa Messi din ya kamo Batistuta ne a wasan su kafin wannan da kasar Venezuela.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel