Ni daga babban gida na fito ba irin Okorocha ba - Inji Eze Madumere

Ni daga babban gida na fito ba irin Okorocha ba - Inji Eze Madumere

Rikicin APC a Jihar Imo yayi kamari har ta kai Mataimakin Gwamnan Jihar Eze Madumere yayi kaca-kaca da Mai gidan na sa Gwamna Rochas Owelle Okorocha wanda yace bai da asali a fadin Jihar.

Ni daga babban gida na fito ba irin Okorocha ba - Inji Eze Madumere
Mataimakin Gwamnan Imo Eze Madumere ya caccaki Okorocha
Asali: Getty Images

Yanzu haka dai bisa dukkan alamu, rigimar Shugaban Gwamnonin na Jam’iyyar APC da Mataimakin sa ya kai intaha inda har ta kai an fara zagin juna. Prince Madumere yace ya fi Rochas Okorocha cancanta ya rike Jihar Imo.

Mataimakin na Gwamna Okorocha yace Gwamnan ba kowan-kowa bane, Madumare yace idan ana maganar sila da asali, ya fi Rochas Okorocha fitowa daga cikin babban gida. Ana duk wannan rigima ne dai saboda zaben 2019.

KU KARANTA: Wasu Jiga-jigan PDP na neman komawa bayan Ganduje a Kano

Kwanaki Gwamna Rochas Okorocha wanda wa’adin sa zai kare a farkon 2019 yace Eze Madumere bai da tasiri a siyasar Imo. Gwamna Okorocha dai yana kokarin kakaba Surukin sa Uche Nwosu a matsayin Magajin sa ne a Jihar.

Prince Madumere ya bayyana cewa rigimar sa da Gwamnan dai ta fara ne a dalilin yin na’am da Surukan sa da ‘Yan uwan sa da ake kokarin kakabawa a mulki. Madumare yace yana bayan Talakawan Gari da ke neman ayi adalci.

Mataimakin Gwamnan yayi wannan jawabi ne a gaban wasu manyan ‘Yan APC a Hedikwatar Jam’iyyar inda yace ba zai tsaya yana kallo Gwamna Okorocha ya maida mulkin Jiha gadon 'Yan gidan sa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel