‘Yan Majalisan Tarayyar Najeriya su na yi wa kudirin zabe garambawul

‘Yan Majalisan Tarayyar Najeriya su na yi wa kudirin zabe garambawul

Mun samu labari a jiya daga gidan Talabijin na Channels TV cewa kudirin da ke kokarin yi wa tsarin zabe garambawul a Najeriya ya shiga mataki na biyu a Majalisar Wakilan Tarayya bayan an dawo aiki.

‘Yan Majalisan Tarayyar Najeriya su na yi wa kudirin zabe garambawul
Ana neman yi wa tsari da dokokin zabe garambawul a Najeriya
Asali: UGC

A Ranar Talata ne ‘Yan Majalisar Tarayya su ka kwankwashi kudirin da zai kawo gyara a harkar zaben kasar nan. Shugaban Majalisa Rt. Hon. Yakubu Dogara ya bayyana cewa yau Laraba ne za a sake duba kudirin domin yi masa gyare-gyare.

A baya dai Majalisa tayi wa dokar zaben gyara amma Shugaban kasa Buhari ya ki sa hannu saboda an canza yanayin gudanar da zaben Kasar. Shugaba Buhari dai ya nuna cewa bai yadda a fara yin zaben Majalisu kafin na Shugaban kasa ba.

KU KARANTA: Atiku za mu zaba a 2019 inji Inyamurai da ke Arewacin Najeriya

Mako guda kenan yanzu da Majalisar Dattawa ta amince da irin wannan kudirin a zaman da tayi. Sanata Sulaiman Nazif wanda shi ne Shugaban wannan kwamiti na harkar zabe yace sun gama yin duk wata kwaskwarima da za ayi wa wannan kudiri.

Ana sa rai dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu idan an mika masa kudirin a gaban sa bayan Majalisar Wakilai da ta Dattawa sun zaftare duk inda ake tunani za a samu cikas kamar shiga cikin batun zaben kananan Hukumomin kasar.

Kun ji cewa Sanatocin Najeriya sun ziyarci batun kudin da Gwamnatin Najeriya ta ke kashewa kan tallafin man fetur. Ana kishin-kishin din cewa NNPC tana kashe makudan Daloli kan tallafin mai a boye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel