Takai, Wali da wasu jiga-jigan PDP a Kano na shirin sauya sheka zuwa APC

Takai, Wali da wasu jiga-jigan PDP a Kano na shirin sauya sheka zuwa APC

Mun fara jin kishin-kishin din cewa Malam Salihu Sagir Takai wanda sau 2 yana neman takarar Gwamna a Jihar Kano na iya ficewa daga Jam’iyyar adawa ta PDP bayan da ya rasa takarar wannan karo.

Takai, Wali da wasu jiga-jigan PDP a Kano na shirin sauya sheka zuwa APC
Watakila Takai ya koma bangaren Shekarau da Ganduje a Kano
Asali: Twitter

Jaridar Prime Time News ta bayyana cewa akwai yiwuwar Salihu Sagir Takai da wasu Kusoshi na Jam’iyyar PDP su koma APC a Jihar Kano. Hakan na zuwa ne bayan INEC ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin ‘Dan takara.

A jiya ne dai Hukumar zabe na kasa ta mikawa Surukin tsohon Gwamna Kwankwaso watau Abba K Yusuf takardar shaidar tsayawa takarar Gwamna a Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar PDP wanda hakan sam bai yi bangaren Takai dadi ba.

KU KARANTA: Uwar Jam’iyya za ta zabi wanda zai yi takarar tsakanin Surukin Kwankwaso da Takai

Kamar yadda mu ka ji, wannan mataki da aka dauka ya sa jiga-jigan Jam’iyya irin su Aminu Wali da sauran wadanda su kayi takaran Gwamna a karkashin PDP a Jihar Kano su ke tunanin komawa wajen Gwamna Abdullahi Ganduje.

Majiyar ta tabbatar da cewa an kira wani taro cikin dare jiya a gidan Ambasada A. Wali inda manyan PDP wanda ba su tare da bangaren ‘Yan Kwankwasiyya su ka halarta. Ba mamaki dai kusoshin na PDP su tsere zuwa APC kafin zaben 2019.

Abba Yusuf Suruki ne wajen Sanata Rabiu Kwankwaso kuma shi ya lashe zaben fitar da gwani da aka yi kwanaki a gidan tsohon Gwamnan. Sauran ‘Yan takaran dai ba su amince da wannan zabe ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel