Tsatstsamar dangantaka: Kaakakin wani gwamna ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda

Tsatstsamar dangantaka: Kaakakin wani gwamna ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda

Kaakakin gwamnan jahar Akwa Ibom Udom Emmanuel, Joe Iniodu ya jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda ta hanyar ajiye aikinsa, tare da yanke duk wata alakar aiki dake tsakaninsa da gwamnatin jahar Akwa Ibom.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Joe ya yi murabus ne tun kimanin sati biyu da suka gabata, kuma ya kwashe tsawon lokacin yana rike da wannan mukami, tun zamanin tsohon gwamnan jahar Godswill Akpabio.

KU KARANTA: Magiya: Ka shiga tsakanina da masu neman halaka ni – Dino Melaye ga Buhari

Sai dai ajiye aikin da Joe ya yi ba shine farau ba, saboda a yan kwanakin ma an samu hadiman Gwamna Udom Emmanuel da suka yi raba gari da maigidannasu, musamman wadanda suke nan tun zamanin tsohon gwamna Akpabio.

Wadannan hadimai na gwamnan jahar Akwa Ibom sun yi murabus ne tun bayan da tsohon gwamnan ya yi wankan tsarki irin na siyasa, inda ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC a watan Agustan da ya gabata.

Sai dai Joe yace “Ajiye aikina ba shi da nasaba da kokarin bata ma gwamnatin suna, na ajiye aikin ne don kashin kaina ba wai don wani bukata ta siyasa ba.” Inji shi, don haka yace kada a siyasantar da batun ajiye aikin nasa.

Joe ya cigaba da fadin “Rahoton da ake yadawa na cewa wai na ajiye aiki ne saboda an tilasta min na yi rubutun batanci ne ga tsohon gwamna Sanata Godswill Akpabio ba gaskiya bane, bashi da tushe balle makama, babu wanda ya taba bani wannan umarni.

“Bari na kara jaddada cewa na ajiye aiki ne don radin kaina, babu wanda ya tilasta min ajiyewa, abnda na sani kawai shine a yayin da aka kada gangar siyasa, babu yadda za’ayi na yi aikina ba tare da na bata ma wasu mutanen da nake ganin mutuncin rai ba.

“Domin kauce ma wannan rashin halascin ne yasa na ajiye aikina, domin na koma gefe na kalli yadda zata kaya tsakanin yan siyasar, tare da bada gudunmuwa ba tare da nuna bangaranci ba. Ina sake jaddada ina ganin girma Gwamna Emmanuel Udom.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel