Zaben 2019: Wanda bai san menene siyasa ba ne kadai zai goyi bayan Buhari

Zaben 2019: Wanda bai san menene siyasa ba ne kadai zai goyi bayan Buhari

- Wani malamin addini ya fadi ajin mutanen da kadai za su zabi Buhari

- Wanda bai san menene siyasa ba ne kadai zai goyi bayan Buhari

Daya daga cikin manyan malaman addinan kirista a kasar nan kuma shugaban rukunin majami'un Mount Zion Faith Global Liberation Ministry Inc.( a.k.a. By Fire By Fire) da ke a garin Nnewi, jihar Anambra mai suna Bishop Abraham Udeh ya yi kaca-kaca da masoya Muhammadu Buhari.

Zaben 2019: Wanda bai san menene siyasa ba ne kadai zai goyi bayan Buhari
Zaben 2019: Wanda bai san menene siyasa ba ne kadai zai goyi bayan Buhari
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kulle-kullen da Atiku keyi don samun goyon bayan Yarbawa a 2019

Bishop din wanda a jiya ya zanta da manema labarai, ya bayyana cewa dukkan masu son Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya zarce to lallai shi babban makiyin demokradiyya ne.

Legit.ng ta samu cewa ya kuma kara da cewa kusan dukkan shika-shikai da sharuddan demkradiyya shugaban kasar da gwamnatin sa sun sa kafa sun shure su a lokuta da dama a lokacin mulkin su.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a wani salo na siyasa da girmamawa, ya yi ta kwararawa tsohon shugaban kasar nan kuma na farko tun bayan dawowar mulkin farar hula a jamhuriya ta hudu, Cif Olusegun Obasanjo.

Shugaba Buhari, wanda yake jawabi ga sabbin jakadodjin kasashe da dama da aka turo Najeriya ciki hadda na kasar Namibia, ya bayyana cewa Cif Obasanjo da kuma marigayi Muritala Mohammed sun yi namijin kokari wajen samarwa kasar Namibia 'yancin kai daga turawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel