Yaki-dan-zamba ne: Shugaba Buhari ya yabawa Obasanjo kan namijin kokarin sa

Yaki-dan-zamba ne: Shugaba Buhari ya yabawa Obasanjo kan namijin kokarin sa

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a wani salo na siyasa da girmamawa, ya yi ta kwararawa tsohon shugaban kasar nan kuma na farko tun bayan dawowar mulkin farar hula a jamhuriya ta hudu, Cif Olusegun Obasanjo.

Shugaba Buhari, wanda yake jawabi ga sabbin jakadodjin kasashe da dama da aka turo Najeriya ciki hadda na kasar Namibia, ya bayyana cewa Cif Obasanjo da kuma marigayi Muritala Mohammed sun yi namijin kokari wajen samarwa kasar Namibia 'yancin kai daga turawa.

Yaki-dan-zamba ne: Shugaba Buhari ya yabawa Obasanjo kan namijin kokarin sa
Yaki-dan-zamba ne: Shugaba Buhari ya yabawa Obasanjo kan namijin kokarin sa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dalilin da yasa nike luwadi - Matashi mai shekara 23

Legit.ng ta samu cewa a cikin 'yan kwanakin nan dai dangantaka a tsakanin shugabannin ta dan yi tsami biyo bayan juyawar baya ga shugaba Buhari da shi Obasanjo yayi a zaben 2019 mai zuwa.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Ogun dake a shiyyar kudu maso yammacin kasar nan kuma dan jam'iyyar APC mai mulki, Sanata Ibikunle Amosun ya karyata dukkan jita-jitan da ake yadawa na cewa shi ya sauya sheka daga jam'iyyar APC.

Gwamnan wanda yanzu haka yake kan ida wa'adin mulkin sa na biyu kuma na karshe, ya yi wannan karin hasken ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun sa kuma kwamishinan harkokin yada labarai, Otunba Adedayo ya fitar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel