Rikicin takarar PDP a Kano: INEC ta bawa surikin Kwankwaso takardar shaidar takara a PDP, hotuna

Rikicin takarar PDP a Kano: INEC ta bawa surikin Kwankwaso takardar shaidar takara a PDP, hotuna

A yayin da rahotanni su ka kama baza gari cewar jam'iyyar PDP ta maye sunan Abba K. Yusuf, surikin Kwankwaso, da na Mallam Salihu Sagir Takai, a matsayin dan takarar gwamnan Kano, sai ga shi hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi akasin hakan.

A wani rahoto da Legit.ng ta ci karo da shi, an ga Abba K. Yusuf na nuna takardar shaidar zama dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar PDP da hukumar INEC ta ba shi.

An fara bayyana Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan Kano a PDP bayan surukinsa Kwankwaso ya gudanar da zaben fitar da dan takara a gidansa dake Kano.

Rikicin takarar PDP a Kano: INEC ta bawa surikin Kwankwaso takardar shaidar takara a PDP, hotuna
Abba K. Yusif
Asali: Facebook

Rikicin takarar PDP a Kano: INEC ta bawa surikin Kwankwaso takardar shaidar takara a PDP, hotuna
Takardar INEC
Asali: Facebook

Sai dai ragowar 'yan takarar kujerar gwamnan Kano a jam'iyyar ta PDP sun yi watsi tare da yin Alla-wadai da zaben fitar da dan takarar da Kwankwaso ya gudanar.

DUBA WANNAN: Bidiyon Ganduje na karbar daloli: Dalilin da ya sa ba zamu iya daukan wani mataki ba - APC

Wannan rikici ne ya kai ga uwar jam'iyyar PDP ta shiga tsakani tare da gudanar da wani zaben cikin gida da Malam Salihu Sagir Takai ya lashe sannan aka ba shi tuta a matsayin halastaccen dan takara

Batun bawa Yusuf takardar shaidar zama dan takara da INEC ta yi zai zama "ta leko ta koma" ga Takai.

Sai dai ya zuwa yanzu ba a ji wani martani ko raddi daga jam'iyyar PDP da bangaren Takai ba a kan wannan sabon al'amari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel