Yan sanda sun kama gagaruman yan fashi da makami 4 a Jigawa sun kwato bindigogi

Yan sanda sun kama gagaruman yan fashi da makami 4 a Jigawa sun kwato bindigogi

Rundunar yan sandan jihar Jigawa a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba sun ce sun kama wasu manyan yan fashi hudu a karamar hukumar Gwaram dake jihar.

Kwamishinan ýan sandan jihar, Mista Bala Senchi, ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Dutse, sannan ya bayyana cewa ýan ta’addan sun addabi mazauna yankin.

Senchi ya bayyana cewa jami’an rundunar yan sandan Federal Special Anti-Robbery Squad (FSARS) ne suka kama su a ranar 26 ga watan Satumba bayan sun samu tsegumi daga majiya abun dogaro.

Yan sanda sun kama gagaruman yan fashi da makami 4 a Jigawa sun kwato bindigogi
Yan sanda sun kama gagaruman yan fashi da makami 4 a Jigawa sun kwato bindigogi
Asali: Depositphotos

Ya bayyana cewa za’a hukunta hudu daga cikin tawagar da suka tsere, inda ya bayyana cewa laifinsu ya saba ma sashi na 96 da 296 na doka.

KU KARANTA KUMA: 2019: Tsohon jigon APC ya yaba da sabon mukamin da Atiku ya ba Saraki

Senchi ya kara da cewa tawagar sun sha kai hare-hare da dama a kauyukan Ranbazau, Yadda da kuma Sara dake yankin inda suka sace dukiyoyi da kudade.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato harda bindigogi na gargajiya da ak47 guda biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel