Atiku za mu zaba a 2019 - Inyamurai dake Arewacin Najeriya

Atiku za mu zaba a 2019 - Inyamurai dake Arewacin Najeriya

Wata kungiyar kabilar Ibo ta Pan-Igbo Think Tank Group da ta fi shahara da sunan Izu Umunna Cultural Association of Nigeria, tun a yanzu ta fayyace wanda za ta kadawa kuri'u cikin 'yan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

'Kungiyar ta bayyana cewa mambobin ta 'yan kabilar Ibo dake Arewacin Najeriya ba bu wanda za su kadawa kuri'un su a yayin babban zabe face dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, kungiyar da sanadin shugabanta, Patrick Ugo Ihekuna, ta bayyana cewa Inyamurai dake yankin Arewacin Najeriya ba su da wani zabi da ya wuce Atiku a yayin zabe na 2019.

Atiku za mu zaba a 2019 - Inyamurai dake Arewacin Najeriya
Atiku za mu zaba a 2019 - Inyamurai dake Arewacin Najeriya
Asali: Depositphotos

Yake cewa, ko shakka ba bu Inyamurai dake yankin Arewacin Najeriya za su yiwa Wazirin Adamawa sakayya da goyon bayan su kuma su na kyautata zato wannan goyon baya zai yi tasirin gaske a yayin babban zaben na badi.

KARANTA KUMA: Goyon baya na Obasanjo ga Atiku ba zai tasiri ba a Zaben 2019 - RBM

Kungiyar a yayin jaddada goyon bayan ta ga tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, ta kuma yabawa masa tare da jam'iyyar sa ta PDP dangane da zaɓi tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi a matsayin abokin tafiya da wanda zai masa mataimaki.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta bayar da sanarwar wani mummunan hari na 'yan Bindiga da ya salwanta da rayukan Matafiya 5 a mahaifar Atiku, watau jihar Adamawa.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel