Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 4 da suka turo Najeriya

Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 4 da suka turo Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi maraba da sabbin jakadun da gwmnatocin manyan kasashen duniya guda hudu da suka turosu Najeriya don jagaorantar ayyukan ofisoshin jakadancinsu dake kasar tare da cigaba da tafiyar da alakae diflomasiyya dake tsakanin kasashen.

Buhari ya karbi bakoncin jakadun ne a ranar Talata 16 ga watan Oktoba a fadar gwamnatin Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja, inda jakadun kasashen Japan, Rasha, UAE da Brazil suka mika masa shaidar nadasu wannan mukami.

KU KARANT: Ta’aziyyar Hauwa Liman: Yarinyar kirkice – Inji Mahaifinta

Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 5 da suka turo Najeriya
Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 5 da suka turo Najeriya
Asali: UGC

Legit.ng ta ruwaito jakadun sun hada da Yutaka Kikuta daga kasar Japan, Alexey Shebarsin daga kasar Rasha, Richardo Guerra DE Araujo daga kasar Brazil, sai kuma Fahad Obaid Mohammed Obaid Altaffag daga kasar UAE Dubai.

A wani labarin kuma fadar shugaban kasa ta musanta rahoton dake yawo na cewa wai gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hana wasu manyan mutane guda hamsin ficewa daga Najeriya saboda tuhume tuhumen da take musu da suka shafi cin hanci da rashawa.

Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 5 da suka turo Najeriya
Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 5 da suka turo Najeriya
Asali: Facebook

Kaakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a ranar Lahadi, 14 ga watan Oktoba, don yin bayani dalla dalla game da sunayen da wata jarida ta buga na cewa sune mutanen da gwamnati ta yi ma wannan takunkumi.

“Ina tabbatar muku babu wani jerin sunayen mutane da aka hana fita, kuma bamu muka fitar da sunayen ba, yawancin sunayen da aka ambata sunaye ne da an san da maganan shari’unsu, don haka fitar da sunayensu ko akasin haka ba zai kara musu nauyi laifi ba.” Inji shi.

Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 5 da suka turo Najeriya
Buhari ya amshi sabbin jakadun kasashen Duniya 5 da suka turo Najeriya
Asali: Facebook

Amma Malam Garba yayi Karin haske game da sabuwar dokar da gwamnati ta samar ‘EO 6’

“Dokar EO 6 za ta sauya fasalin yaki da rashawa a Najeriya, manufarta itace don kara sauri ga shari’un da ake yi da suka shafi yaki da rashawa, tare da rage adadin lokacin da ake dauka ana gudanar da shariar.” Inji shi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel