Ta’aziyyar Hauwa Liman: Yarinyar kirkice – Inji Mahaifinta

Ta’aziyyar Hauwa Liman: Yarinyar kirkice – Inji Mahaifinta

Malam LIman mahaifin ma’aikaciyar jinyar nan da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta kasha, Hauwa Liman ya bayyana alhininsa da ta iyalansa, dangi da ma yan uwa da abokan arziki, inda yace sun kadu matuka da wannan lamari.

Mahaifn ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da gidan rediyon BBC Haus a ranar Talata 16 ga watan Oktoba, inda ya bayyana marigayiyar a matsayin yarinyar kirki wanda bata da matsala da kowa, tana zaman lafiya da kowa.

KU KARANTA: Wata Mata ta dandana kudarta bayan Kotu ta kamata da laifin safarar yan mata

Majiyar Legit.ng ta jiyo shi yana cewa: “Gaskiya bamu ji dadi ba, abin ya damemu, abokananmu, duk muna jin zafin wannan abu, damuwa sosai, ita mai kirkice, kuma bata gaba da kowa.”

Ta’aziyyar Hauwa Liman: Yarinyar kirkice – Inji Mahaifinta
Hauwa Liman
Asali: Twitter

Haka zalika Malam Liman ya cigaba da jawabin cewa: “Ita dai ta yi aikin jama’a, tana aikin lura da masu haihuwa, watau unguwar zoma, kuma tana taimaka ma jama’a sosai, da kuma yara kanana. Ina kira ga kungiyar Boko Haram da su sake wanda suke hannunsu, domin basu da wani laifi, saboda taimako suka je suke yi aka kama su.” Inji shi.

Rahotanni sun nuna mayakan na Boko Haram sun bindige Hauwa ne a daidai lokacin da suka tilasta ta tsugunna tana sanye da farin Hijabi, hannayenta na daure a cikin hijabin, daga nan suka dirka mata bindiga a kai.

Bangaren Boko Haram dake karkashin jagorancin Abu Mus’ab Albarnawi ne suka yi awon gaba da Hauwa Liman ne a watan Maris yayin da suke duba marasa lafiya a wani sansani dake zagaye da Sojoji a garin Rann, tana aiki ne da kungiyar bada agaji na duniya, wato Red Cross.

Sauran wadanda aka sace tare da Hauwa akwai Saifura Khorsa wanda suka kasheta a kwanakin baya, sai kuma Alice Loksha, wanda har yanzu tana hannun mayakan na Boko Haram dake da alaka a kungiyar ISIS.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel