APC Bauchi: Ko dai ku sake sabon zaben fidda gwami ko ku mayar min da kudina - Yar takara

APC Bauchi: Ko dai ku sake sabon zaben fidda gwami ko ku mayar min da kudina - Yar takara

- Wata yar takarar kujerar majalisar dokoki ta jihar Bauchi, ta bukaci shuwagabannin jam'iyyar APC na kasa da su sake sabon zabe a jihar

- Hon. Aishatu Haruna wacce aka fi sani da 'Gimbiya' ta ce idan jam'iyyar ba zata sake gudanar da zaben ba, to ta mayar masu da kudin da suka kashe

- Yar takarar, ta bayyana cewa Gwamna Mohammed Abubakar, ya yi alkawarin ganawa da 'yan takarar amma har yanzu bai waiwaye su ba

Yar takarar kujerar majalisar dokoki ta jihar Bauchi a karkashin jam'iyyar APC, wacce ta sha kasa a zaben fitar da gwani da jam'iyyar ta gudanar, ta yi kira ga shuwagabannin jam'iyyar na kasa da su sake gudanar da zaben fitar da gwani na jihar ko kuma su mayar mata da kudin form na sha'awar takara da ta siya.

Da ta ke jawabi ga manema labarai a ranar Talata a Bauchi, yar takarar, Hon. Aishatu Haruna wacce aka fi sani da 'Gimbiya', wacce ta tsaya takara a mazabar Zungur/Galambi a majalisar dokoki ta jihar, ta bayyana cewa babu wani zabe da aka gudanar a jihar, amma daga bisani jam'iyyar ta bayyana sunayen 'yan takarar da take so a matsayin wadanda suka lashe zaben.

A cewar ta: "Sun sayar mana da fom, sun tantance mu tare da tabbatar da cewa babu wata matsala, amma sai gashi basu bamu wata dama a matsayin 'yan takara na shiga zaben ba. A zahirin gaskiya ma babu wani zabe da ya gudana, kawai dai sun zabi wadanda suke so.

APC Bauchi: Ko dai ku sake sabon zaben fidda gwami ko ku mayar min da kudina - Yar takara
APC Bauchi: Ko dai ku sake sabon zaben fidda gwami ko ku mayar min da kudina - Yar takara
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: IGP Idris ya gargadi 'yan sanda akan tsare mai laifi sama da awanni 48

"Don haka ne muke rokon shelkwatar jam'iyyar na kasa da kuma shugaban kasa Buhari da su sa baki a wannan maganr don tabbatar da yin adalci a garemu. Mu kawai abun da muke so, a soke wannan zabe, ko kuma a mayar mana da kudadenmu."

Yar takarar, wacce ta bayyana cewa Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar, bayan kammala zaben fitar da gwanin, ya yi alkawarin ganawa da 'yan takarar da lamarin ya sha, ta ce har zuwa wannan lokaci, bai ko waiwaye su don cika alkawarin da ya dauka ba.

"Har zuwa yanzu, ba a sanar damu lokacin da gwamna zai gana da mu ba. Ya zamar masa dai wajibi ya ganmu a matsayin na 'yan takarar jam'iyya don amayar masa da abubuwan da ke cikinmu. Idan kuma bamu ji daga gareshi ba na tsawon kwanaki, to zamu dauki mataki na gaba," kamar dai yadda ta yi barazana.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel