Barakar PDP: Salihu Takai da Abba Yusuf za su kara a zaben 2019

Barakar PDP: Salihu Takai da Abba Yusuf za su kara a zaben 2019

Yayin da ake shirin zaben 2019, har yanzu dai ba a san takamamen ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar PDP mai adawa ba. Daily Trust tayi dogon sharhin abin da ya faru a Jihar.

Barakar PDP: Salihu Takai da Abba Yusuf za su kara a zaben 2019
Ba a san wanda zai rikewa PDP tuta tsakanin Salihu Takai da Abba Yusuf ba
Asali: UGC

Bangaren Sanata Masud Jibril El-Doguwa wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar PDP da aka yi waje da shi kwanaki ya bayyana cewa Salihu Sagir Takai ne ‘Dan takarar su na Gwamnan Jihar Kano a zaben 2019 ba Abba Kabir Yusuf ba.

Abba K. Yusuf dai Suruki ne wajen tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso kuma shi ne ya lashe zaben fitar da gwani da aka yi kwanaki a gidan tsohon Gwamnan. Hakan ta sa ‘Yan takaran su kayi watsi da wannan zabe da aka yi.

A dalilin rashin amincewa da sahihanci zaben da aka gudanar ne ya sa manya da Shugabannin PDP na Jihar Kano su ka zauna domin yi wa kan su masalaha. Sai dai shugabannin Jam’iyyar sun rasa yin itiffafaki a kan ‘Dan takara.

KU KARANTA: Babu Kwankwaso a cikin jagororin yakin neman zaben Atiku

Wannan dai ya sa Shugabannin kananan Hukumomi na PDP a Jihar Kano su ka kada kuri’a tsakanin su inda Salihu Takai yayi nasara da kuri’u 20. Sadiq Aminu Wali ya kuma samu kuri’u 16 yayin Ibrahim Little ya samu 2 rak.

Wannan zabe da shugabannin Kananan Hukumomin PDP na Kano su kayi ne ya sa bangaren na Doguwa su ka zabi Takai a matsayin ‘Dan takaran su. Su kuma dai bangaren Kwankwasiyya sun ce ba sun kowa ba sai Abba K. Yusuf.

Yanzu haka dai Uwar Jam’iyyada ke Abuja ba ta ce komai ba inda ake tunani ita za ta raba gardama ta mika sunan ‘Dan takaran ta a gaban Hukumar zabe na kasa a makon nan kafin lokaci ya kure mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel