Magiya: Ka shiga tsakanina da masu neman halaka ni – Dino Melaye ga Buhari

Magiya: Ka shiga tsakanina da masu neman halaka ni – Dino Melaye ga Buhari

Wakilin al’ummar mazabar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya kai kukansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan wani yunkuri da yace a yanzu haka ake yi don ganin an halaka shi, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Melaye ya bayyana ma Buhari cewa rundunar Yansandan jahar Kogi da hadin gwiwar gwamnatin jahar Kogi a karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello ne suke shirya masa wannan makarkashiyar.

KU KARANTA: Ya kamata EFCC ta yi taka tsantsan wajen kama Fayose – Shugaban jam’iyyar PDP

Cikin wasikar da ke dauke da kwanan wata na 13 ga watan Oktoba, Melaye yace rundunar Yansandan Najeriya ta janye masa Yansandan dake gadinsa tun a watan Afrilun bana, wanda hakan ya kara jefa rayuwarsa cikin hadari.

Magiya: Ka shiga tsakanina da masu neman halaka ni – Dino Melaye ga Buhari
Melaye
Asali: UGC

Da wannan ne Sanata Dino Melaye ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma babban kwamandan hafsoshin tsaron Najeriya, da ya baiwa babban sufetan Yansandan Najeriya, umarnin ya dawo masa da Yansandan dake gadinsa, domin kuwa a matsayinsa na Sanata ya cancanci a bashi tsaro.

Bugu da kari baya ga mika wannan wasikar koke ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Melaye ya aike da kwafin wasikar ga Alkain Alkalai, kungiyar kare hakkin bil adama ta duniya Amnesty International (AI), Kungiyar kasashen turai (EU), Gwamnatin kasar Amurka, Canada da Jamus, majalisar dinkin duniya, kungiyar kasashen yammacin Afirka da kungiyar kasashen nahiyar Afirka.

Sai dai rundunar Yansandan jahar Kogi ta musanta zarge zargen da Sanatan yayi, inda ta bakin kaakakinta, DSP William Ovye Aya ta bayyana cewa maganganun da Dino yayi karya ne, kuma kokarin bata mata suna kawai yake yi.

”Rundunar Yansandan jahar Kogi ta dade tana neman Dino Melaye ruwa a jallo, saboda tuhumar aikata laifin kisan kai, don haka kwamishinan Yansandan jahar Kogi na kira ga Dino da ya mika kansa ga Yansanda don amsa laifin da ake tuhumarsa a kai.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel