Har yanzu ban yarda cewar ýata ta mutu ba – Mahaifiyar Hauwa Liman

Har yanzu ban yarda cewar ýata ta mutu ba – Mahaifiyar Hauwa Liman

Mahaifiyar ma’aikaciyar agaji da ýan ta’addan Boko Haram suka kashe ta ce bata yarda cewar ýarta ta mutu ba.

Mama Hauwa kamar yadda mutane ke kiranta ta ce ta yi imanin cewa har yanzu ýarta na nan da ranta kuma ba lallai bane an kashe ta kamar yadda ýan ta’addan suka yi barazana.

Da take Magana a lokacin wata zangazanga kan zargin kashe Hauwa, wata ýar asalin jihar Borno, Barista Fatima Abdullahi ta ce Mama Hauwa bata yarda ba har yanzu.

Har yanzu ban yarda cewar ýata ta mutu ba – Mahaifiyar Hauwa Liman
Har yanzu ban yarda cewar ýata ta mutu ba – Mahaifiyar Hauwa Liman
Asali: UGC

“Na yi Magana da ita jiya, ta fada mun cewa ta ji wai an kashe Hauwa,” inji Fatima.

“Mun sake Magana da safen nan, ta ce ba zai yiwu ace Hauwa ta mutu ba.”

"A matsayinta na uwa bata yarda cewa Hauwa ta mutu ba. Har yanzu tana musantawa, tare da burin cewa ýarta zata dawo. Ta fada mun har yanzu tana buri da addu’an dawowar ýarta.

“Ya kamata mu yarda cewa a wannan kasar rayuwar kowa na da muhimmanci, kowace uwa bazata damu ba idan har aka karar da CBN domin ceto ýarta. Mun yi matukar bakin ciki da kisan Hauwa kuma an bamu kunya," Inji ta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An tsaurara matakan tsaro a Ado-Ekiti yayinda ake rantsar da Fayemi a yau

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa shugaban kungiyar Bring Back Our Girls group, Obiageli Ezekwesili, ta sha kuka a wajen zanga-zangar da ýan kungiyar suka yi a ranar Talata, 16 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel