Karshen duniya: An kama wasu matasa maza da mata 14 suna tika rawa zigidir a jihar Kebbi

Karshen duniya: An kama wasu matasa maza da mata 14 suna tika rawa zigidir a jihar Kebbi

- 'Yan banga sun kama wasu matasa maza da mata 14 sun tika rawa tsirara a jihar Kebbi

- An kama matasan ne a karkashin wata gado kusa da rafi tare da kayan kidansu cikin maye

- Kotu ta bayar da umurnin basu masauki a gidan yari kafin a zartas musu da hukunci

Wata kotun Majistare da ke zamanta a Birnin Kebbi ta Jihar Kebbi ta bayar da umurnin tsare wasu matasa maza 9 da mata 5 da aka kama sun tika ruwa tsirara a karkashin wani gada a jihar.

Alkaliyar Kotun, Halima Abubakar wadda ta ke jagorancin Shari'ar da kungiyar 'yan banga da ke jihar suka kawo ta bayar da umurin a bawa matasan masauki a gidan yari.

Karshen duniya: An kama wasu matasa 14 suna tika rawa tsirara a jihar Kebbi
Karshen duniya: An kama wasu matasa 14 suna tika rawa tsirara a jihar Kebbi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Magudin Jarabawa: Gwamnati ta maka dan takarar gwamnan PDP a kotu

Ana tuhumar matasan 14 da aikata laifukan hadin baki wajen aikata laifi, tayar da hankalin al'umma, makirci da yiwa wani rauni wanda duk sun ci kara da sashi na 97, 183, 327, 66 da 246 na Penal Code.

A cewar mai gabatar da karar, Yakubu Mohammed Goge, 'yan banga na Vigilante Group of Nigeria (VGN) reshen jihar Kebbi ne suka kama yaran inda suke tika rawa tsirara tare da kayan kidansu a cikin maye.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta kawo muku cewar wata yarinya mai shekaru 20, Amina Hassan a jihar Kaduna ta shigar da mahaifinta kara kotu saboda ya ki aura mata masoyinta da suka dade suna soyaya.

Amina ta roki kotun ta umurci mahaifinta ya daura mata aure da saurayin, idan kuma bai amince ba kotun tayi daura mata auren ko da baya so.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel