IGP Idris ya gargadi 'yan sanda akan tsare mai laifi sama da awanni 48

IGP Idris ya gargadi 'yan sanda akan tsare mai laifi sama da awanni 48

- IGP Ibrahim Idris, ya gargadi jami'an 'yan sanda da su kauracewa tsare mai laifi sama da awannin da dokar kasar ta tanadar, wato awanni 48

- Ya ce duk jami'in da ya kama da aikata laifin, za ayi amfani da albashi da giratutin sa wajen biyan tarar laifin da ya aikata

- Idris ya kuma bukaci asibitoci da su rinka duba marasa lafiyar da suka samu raunukan harbin bindiga, amma su gaggauta kiran jami'an yan sanda

Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda (IGP), Ibrahim Idris, ya gargadi jami'an 'yan sanda da su kauracewa tsare mai laifi sama da awannin da dokar kasar ta tanadar, wato awanni 48.

A cewarsa, duk wani jami'i da aka kama ya aikata hakan, to kuwa ya keta 'yancin da dokar kasar ta baiwa shi wanda ake tsare da shi.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kwara, Bolaji Fafowora, ya bayyana wannan matsayar da Sifeta Janar na rundunar a Ilorin, a wata zantawa da yayi da manema labarai.

KARANTA WANNAN: Yadda Ezekwesili ta fashe da kuka a lokacin da suke ke zanga zangar kisan Hauwa Liman

Da dumi dumi: Mataimakin shugaban kasa ya tafi kasar Burtaniya don duba lafiyarsa
Da dumi dumi: Mataimakin shugaban kasa ya tafi kasar Burtaniya don duba lafiyarsa
Asali: Depositphotos

Fafowora ya ce duk wani jami'in 'yan sanda da aka kama yana tsare mai laifi ba bisa ka'ida ba to zai fuskanci hukuncin rundunar, za kuma ayi amfani da albashi da giratutin jami'in wajen biyan tarar laifin da ya aikata.

Ya ce rundunar 'yan sanda za tafara biyan kudin tarar ne don kaucewa cin fuska, daga bisani kuma ta cire kudin daga albashi da giratutin jami'in da ya aikata laifin.

Fafowora ya kuma bayyana cewa shi IGP Idris, ya umurci duk wani asibiti da ya ci karo da maras lafiya da ya samu raunuka daga harsashen bindiga, da suka hada da 'yan fashi da makami, to a fara duba lafiyarsa farko, amma daga bisani hukumar asibiti ta gaggauta sanar da ofishin hukumar 'yan sanda mafi kusa don gudanar da binciken da ya dace.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel