Budurwa 'yar shekara 20 tayi karar mahaifinta a kotu domin ya hanata auren masoyinta

Budurwa 'yar shekara 20 tayi karar mahaifinta a kotu domin ya hanata auren masoyinta

- Wata budurwa ta shigar da mahaifinta kara a kotu Shari'a domin ya ki amincewa ta auri masoyinta

- Budurwar mai shekaru 20 a duniya ta roki kotu ta daura mata aure idan mahaifinta ya ki amincewa ya daura mata

- Kotun ta bawa mahaifin da diyarsa makonni biyu su sasanta kansu kafin da dauki mataki

A yau Talata ne, wata budurwa mai shekaru 20 a duniya, Amina Hassan ta yi karar mahaifinta Hassan Adamu a kotun Shari'a da ke Magajin Gari a Kaduna saboda ya ki amincewa ta auri masoyinta.

Budurwar wadda ke zaune da kakarta a Bashama Road da ke Tudun Wada Kaduna, ta bukaci kotu ta umurci mahaifinta ya daura mata aure da masoyinta kamar yadda lauyanta, Ado Ali ya fadawa kotu.

Budurwa 'yar shekara 20 tayi karar mahaifinta a kotu domin hanata auren masoyinta
Budurwa 'yar shekara 20 tayi karar mahaifinta a kotu domin hanata auren masoyinta
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Obasanjo ya fadi yadda gwamnatinsa ta azurta Dangote da wasu manyan attajirai

Ta kara da cewar shekarun ta sun isa tayi aure kuma tana son auren amma mahaifinta ya ki amincewa ta auri wanda ta ke kauna.

"Mahaifinta ya ki amincewa ta auri wanda take so duk da kokarin shawo kansa da nayi hakan yasa na ke rokon kotu daura mata aure idan mahaifinta ya ki amincewa," inji Ado Ali.

Ali ya kuma roki kotu ta bawa Amina da mahaifinta makonni biyu domin su sulhunta kansu inda shima lauyan da ke kare mahaifin Amina, Nasir Abdullahi ya goyi bayan wannan rokon.

Alkalin kotun, Malam Dahiru Lawal ya amsa rokon lauyoyin inda ya kara da cewar mahaifin yarinyar yana da damar tantance wadda mutumin da diyarsa za ta aura amma bashi da ikon tilasta mata auren wadda ba ta so a shari'ance.

Daga karshe ya umurci lauyan da ke kare wanda akayi kararsa da ya gabatar da mahaifin yarinyar a kotu a ranar 29 ga watan Oktoba domin cigaba da sauraron karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel