Zaben Buhari a 2019 tamkar kunar bakin wake ne - Aminu Tambuwal

Zaben Buhari a 2019 tamkar kunar bakin wake ne - Aminu Tambuwal

- Aminu Waziri Tambuwal ya ce zai zama kamar kunar bakin wake idan har yan Nigeria suka bari Buhari ya zarce mulki a 2019

- Ya ce tun bayan zaben fitar da gwani na PDP, ya dau kudurin marawa Atiku Abubakar baya don lashe zaben shugaban kasar

- Tambuwal ya ce basa fatan mulkin Buhari ya ci gaba, bayan ranar 29 ga watan Mayun 2019

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce zai zama kamar kunar bakin wake idan har yan Nigeria suka bari shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce mulki a 2019.

Tambuwal, wanda na daya daga cikin yan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya yi zargin cewa ba Buhari ne ke da ikon ragamar kasar ba.

Ya yi wannan jawabi ne a Abuja a lokacin da kwamitin sulhu da jam'iyyar PDP ta kafa ya kai masa ziyara a gidansa na Maitama (Abuja).

Ya ce: "Ina so in kara tabbatar maku, mambobin jam'iyyarmu maza da mata dama daukacin yan Nigeria cewa a shirye nake, kuma zan yi aiki tukuru don ganin jam'iyyarmu ta samu nasarar lashe zaben 2019.

Zaben Buhari a 2019 tamkar kunar bakin wake ne - Aminu Tambuwal
Zaben Buhari a 2019 tamkar kunar bakin wake ne - Aminu Tambuwal
Asali: Facebook

Shirye shirye sun yi nisa, na yadda zamu tabbatar da wannan kudiri namu kuma tun bayan kammala zaben fitar da gwani na bayyana kuduri na marawa wanda ya yi nasara baya. Muna goyon bayan Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar 100 bisa 100. Ninkomai ya shige a wajena, aikin da ke gabanmu shine na ke ma shiri.

KARANTA WANNAN: Na shirya tsaf don mika kaina ga hukumar EFCC dauke da bargo, fulo da kayan bacci - Fayose

"Mun kama hanyar ganin cewa an dinke duk wata baraka da ke cikin jam'iyyar, kuma har yanzu kofa a bude ta ke ga duk wani masoyinmu na shigowa tafiyar don bada gudunmowarsa, a kokarinmu na samun nasarar babban zabe mai zuwa."

A cewar tsohon kakakin majalisar wakilan tarayyar, ba wai kwace mulki a hannun jam'iyyar APC ba ne kudurinsa na yanzu, yana mai cewa "gaba daya batutuwan da muka tattauna, muka tsara, kuma muka amince, a taron mu da wakilan zabe da shuwagabannin jam'iyyar, suna nan yadda suke."

Ya kara da cewa "Shugaban kasa Buhari ba shi mai jan ragamar kasar ba. Zai zama kamar kunar bakin wake idan har aka ce ya dawo mulki na wasu shekaru 4. Don haka bama fatan mulkin nasa ya ci gaba bayan ranar 29 ga watan Mayun 2019."

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel