An raba Auren Wani Malamin Addini da Matar sa kan zargin keta haddi

An raba Auren Wani Malamin Addini da Matar sa kan zargin keta haddi

Da sanadin shafin jaridar Wuzup Nigeria mun samu rahoton cewa, wani Malamin Addini ya na zargin Matar sa, Barakat Adeniyi da keta ma sa haddi inda ya nemi kotu ta shiga tsakanin auren su bayan shekaru biyu da rabi kacal da kulla shi.

Malamin Abdulrazak Adeniyi, ya na zargin Matarsa da bayar da kanta ga tsohon saurayin ta da ya saba kawo mata ziyara a duk lokacin da ya fita kwadago kamar yadda ya saba a kullum.

Bayan watanni biyar da haihuwarta, Barakat ta kuma sake samun wani sabon juna biyu inda ta kauracewa shayar da jaririn ta kamar yadda Adeniya ya bayyana a gaban Kuliya.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari na zargin keta haddin aure ya sanya Adeniyi ya kauracewa iyalinsa domin takaici da kuma bakin ciki na bacin rai.

A na ta korafin, Barakat ta zargi Mai gidan ta da zalunci na rashin kulawa da kuma rashin sauke nauyin igiyar auren su da ta rataya a wuyansa tare da shaidawa kotun cewa tuni ya yanke kaunar da ya saba mata a baya.

An raba Auren Wani Malamin Addini da Matar sa kan zargin keta haddi
An raba Auren Wani Malamin Addini da Matar sa kan zargin keta haddi
Asali: UGC

Alkalin kotun ta al'adu dake birnin Ibadan na jihar Oyo, Suleiman Apanpa, ya cika burikan wannan ma'aurata inda cikin hukuncinsa ya salwantar da auren dake tsakanin su tare da bai wa Barakat dama ta ci gaba da rikon jaririn su har na tsawon shekara daya da rabi.

KARANTA KUMA: Wani Matashi ya yi garkuwa da Mahaifiyar Budurwar sa a jihar Abia

Kazalika Apanpa ya umarci Adeniyi akan ci gaba da biyan N5,000 ga tsohuwar Matarsa a kowane wata domin dawainiya da 'dan sa.

Jaridar Legit.ng kuma ruwaito cewa, da misalin karfe 12.20 na ranar yau ta Talata aka rantsar da sabon zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, tsohon ministan ma'adanai na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel