Shugaba Buhari ya raba ma talakawa N1.5bn a jihar Bauchi

Shugaba Buhari ya raba ma talakawa N1.5bn a jihar Bauchi

A ranar Litinin, 15 ga watan Oktoba ne jami’in shirin tallafa wa talakawa ( CCT) Jibrin Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta raba wa talakawa a jihar Bauchi kudi har naira biliyan 1.5.

Yusuf ya bayyana hakan ne a yayinda wakilan kungiyar manema labarai mata na kasa (NAWOJ) suka kai masa ziyara a ofishin sa da ke garin Bauchi.

Ya ce shirin CCT ta fara raba wadannan kudade ne tun a farkon shekarar nan zuwa wannan lokaci. Sannan yace shirin za ta saka wasu talakawa 2,969 domin su samun wannan tallafi.

Shugaba Buhari ya raba ma talakawa N1.5bn a jihar Bauchi
Shugaba Buhari ya raba ma talakawa N1.5bn a jihar Bauchi
Asali: UGC

A kashe shugaban kungiyar NAWOJ Bulak Afsa ta bayyana cewa sun zo ne domin jinjina wa shirin CCT bisa wannan kokari da suke yi wa talakawa a wannan jiha.

KU KARANTA KUMA: APC ce babban adawar kanta da kanta - Atiku

A baya Legit.ng ta rahoto cewa daraktan kungiyar kamfen din Buhari, Mista Festus Keyamo (SAN) ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ne mafi inganci a nahiyar Afrika.

Keyamo ya bayyana hakan yayinda yake Magana a shirin gidan Channels TV a ranar Litinin, 15 ga watan Oktoba.

Ya ce a cikin kasashe 11 da suka shiga koma bayan tattalin arziki a fadin duniya, Najeriya duk ta fi su bunkasa ta fannin ci gaban kididdiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel