Ana binciken Arda Turan bayan yayi dambe a cikin a gidan rawa

Ana binciken Arda Turan bayan yayi dambe a cikin a gidan rawa

- Arda Turan na iya samun hukuncin daurin shekaru akalla 12 a gidan kaso

- ‘Dan wasan yayi fada ne da wani Mawaki a gidan rawa a Kasar Turkiyya

- A halin yanzu Turan dai ya karyata rade-radin cewa yayi dambe da wani

Ana binciken Arda Turan bayan yayi dambe a cikin a gidan rawa
'Yan Sanda sun soma binciken damben da Arda Turan da yayi da wani
Asali: Getty Images

Mun samu labari cewa ‘Dan wasan nan na tsakiya na ainihin Kungiyar Barcelona ta kasar Sifen ya shiga wani mawuyacin hali inda ake tunani za a iyadaure sa a gidan yari har na tsawon shekaru 12 idan aka same shi da rashin gaskiya.

Ana dai zargin ‘Dan wasan yayi dambe da wani mutumi ne a gidan rawa. Yanzu haka dai idan aka same shi da laifin fada da wani shararren Mawaki mai suna Berkay Sahin, za a iya yanke masa tsawon shekaru na zaman kaso a Turkiyya.

KU KARANTA: Ya koma laifi mako guda bayan an sake shi daga kurkuku

Rahotanni su na yawo cewa ‘Dan wasan yayi dambe ne da wani fitaccen Mawaki da ke Garin Istanbul cikin dare a wani gidan rawa. Yanzu dai Jami’an ‘Yan Sandan Kasar sun soma binciken abin da ya faru tun a makon can da ya gabata.

‘Dan wasan mai shekaru 31 yana taka-leda ne yanzu haka a Kungiyar Basaksehir da ke babban Birnin Istanbul. Kungiyar ta dauko aron ‘Dan wasan ne bayan ya gaza samun damar buga wasa gaba daya a Kungiyar Barcelona ta Kasar Sifen.

Jaridun Turai sun bayyana cewa Matar wannan Mawaki Sahin ce ta jawo fadan inda har ta kai Turan ya zaro bindiga yayi barazanar harbi. A nan-take dai aka zarce da Sahin asibiti bayan ‘Dan kwallon yayi masa mugun rauni a kan karon hancin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel