2019: Sanatoci 42 sunci taliyar karshe, 67 na cikin tsaka mai wuya

2019: Sanatoci 42 sunci taliyar karshe, 67 na cikin tsaka mai wuya

Gabanin zaben 2019 kuma bayan an kammala dukkan zabubbukan fidda gwani, ya bayyana cewa sanatoci 42 sun ci taliyar karshe a majalisa yayinda 67 na cikin tsaka mai wuya a zabe.

Daga cikin wadanda sanatoci 42, 19 sun janye daga takaran ne da kawunansu ko kum sun tafi neman kujeran gwamnan jiharsu. Amma 23 sun sha kasa ne a zaben fidda gwanin mazabarsu.

Wadannan sun kunshi:

Ahmed Sani (APC Zamfara ta gabas), Bukar Abba Ibrahim (APC Yobe ta gabas), Abu Ibrahim (APC Katsina ta kudu), Abubakar Kyari (APC Borno ta arewa ) and Kaka Gabbai (APC Borno ta tsakiya), Jonah Jang (PDP Plateau), Jeremiah Useni (PDP Plateau ta kudu), David Mark (PDP Benue ), Philip Gyunka (PDP Nasarawa ta arewa), Samuel Anyanwu (PDP Imo), Abdulaziz Murtala Nyako (ADC Adamawa ta tsakiya), Usman Bayero Nafada (PDP Gombe ta Arewa).

Sauran sune Kabiru Marafa (APC Zamfara ta tsakiya), Shaaba Lafiagi (PDP Kwara ta arewa), Isiaka Adeleke (PDP Osun ta yamma), Sonny Ogborji (APC Ebonyi Central), John Enoh (APC Cross River Central), Gbolahan Dada (APC Ogun West) and Hope Uzodinma (APC Imo West).

KU KARANTA: Mata ta na kwanciya da tsohon saurayinta a gida na - Wani miji ya koka a gaban kotu

Daga cikin sanatoci 23 da suka kasa a zaben fidda gwanin sune:

Gbenga Ashafa (APC Lagos ta gabas), Lanre Tejuoso (APC Ogun ta tsakiya), Fatima Raji Rasaki (APC Ekiti ta tsakiya), Sola Adeyeye (APC Osun ta tsakiya) and Babajide Omoworare (APC Osun ta gabas), Rilwan Akanbi (APC Oyo ta kudu), Gilbert Nnaji (PDP Enugu ta yamma), Emmanuel Paulker (PDP Bayelsa ta tsakiya), Ben Murray Bruce (PDP Bayelsa West), Fosta Ogola (PDP Bayelsa ta kudu), Ahmed Abubakar (APC Adamawa South).

Sauran sune Rafiu Ibrahim (PDP Kwara ta kudu), Aliyu Sabi Abdullahi (APC Niger ta Arewa), David Umoru (APC Niger ta yamma) da Joshua Dariye (APC Plateau Central) wanda ke cikin kurkuku a yanzu.

Sauran 67 da suka samu nasara a zaben fidda gwani na cikin tsaka mai wuya saboda karawa da zasuyi da jam’iyyun adawa a jihohinsu.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel