Yanzu-yanzu: Dalilin da yasa muka kashe Hauwa Liman - Boko Haram

Yanzu-yanzu: Dalilin da yasa muka kashe Hauwa Liman - Boko Haram

Wata ballin kungiyar Boko Haram mai suna Daular Musulunci da yankin Afrika maso yamma wato ISWAP ta kashe daya daga cikin ma’aikatan kungiyar agajin Red Cross, Hauwa Liman, bayan wa’adin da suka baiwa gwamnatin tarayya ya cika a yau.

Yan ta’addan sunyi alkawarin cewa ba zasu kashe Leah Sharibu ba amma ta zama baiwa har abada. Jaridar The Cable ta samu rahoto.

Yanzu-yanzu: Dalilin da yasa muka kashe Hauwa Liman - Boko Haram
Yanzu-yanzu: Dalilin da yasa muka kashe Hauwa Liman - Boko Haram
Asali: Twitter

A jawabin da yan Boko Haram suka saki, sun bayyana dalilin da yasa suka kasheta da kuma yadda suka kashe ta. A cewarsu,:

“Mun kashe Saifura da Hauwa ne saboda kungiyar ta daukesu yan Ridda saboda sun kasance Musulmai amma sun kafirta tu lokacin da suka zabi aiki da Red Cross. Mu kuma ra’ayinmu, babu banbanci tsakanin Red Cross da UNICEF.

“Idan mun gansu, za mu kashe yan ridda a cikinsu, maza ko mata. Idan muka ga dama mu kashe kafiran ko mu daukesu bayi.”

“Daga yau kuma, Sharibu da Ngaddah sun zama bayinmu. Bisa da akidun, ya hallata a garemu muyi duk abinda muka ga dama da su.”

Hauwa Liman, dalibar Jami’ar Maiduguri ce wacce ke aiki da kungiyar Red Cross a garin Rann, jihar Borno. Sunyi garkuwa da ita tare da abokan aikinta 2 Alice Loksha Ngaddah da Saifura Husseini Ahmed. Kana sun kashe sojoji hudu da yan sanda hudu a harin.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel