Mata ta na kwanciya da tsohon saurayinta a gida na - Wani miji ya koka a gaban kotu

Mata ta na kwanciya da tsohon saurayinta a gida na - Wani miji ya koka a gaban kotu

- Wani malamin Islamiyya, Abdulrazak Adeniyi ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa Barakat

- Abdulrazak ya yi ikirarin cewar Barakat tana kwanciya da tsohon saurayinta duk da cewar tana matarsa

- A bangarenta, Barakat ta amince da bukatar raba auren inda ta ce mijin baya kulawa da ita da hakokinta

A yau Litinin ne wata kotun Majistare da ke zamanta a Mapo da ke Ibadan ta raba datse igiyar aure tsakanin Barakat Adeniyi da Abdulrazak Adeniyi bisa zargin cin amanar aure da rashin kulawa da hakkin aure.

Shugaban kotun, Alhaji Suleiman Apanpa ya bayyana cewar kotun ta raba auren ne saboda dukkan ma'auratan biyu sun nuna cewar ba su sha'awar cigaba da zama da juna.

A karar da Barakat ta shigar da farko, ta zargi mijinta da nuna halin ko in kula gare ta da dan ta inda ta ce ya kwashe makonni biyu bai duba lafiyarta ba ko na dan su.

Mata ta na kwanciya da tsohon saurayinta a gida na - Wani miji ya koka a gaban kotu
Mata ta na kwanciya da tsohon saurayinta a gida na - Wani miji ya koka a gaban kotu
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kuma dai: Sabuwar bidiyo da ke nuna Ganduje na karbar cin hanci ya sake fitowa (Ku Kalla)

A bangarensa, Abdulrazak wadda malamin Islamiyya ne ya karyata zargin da matarsa ke masa inda ya ce ba ta da da'a har ma yana zarginta da bin wasu mazaje.

"Baraka ta dena shayar da yaron mu nono watanni biyar bayan haihuwa ba tare da ta sanar da ni ba.

"Kwatsam kawai sai tsohon saurayinta ya fara kawo mata ziyara a gidana musamman duk lokacin da na fita aiki.

"Bayan qanqanin lokaci Baraka ta sake daukar wani ciki kuma babu kunya sa ta kwashe kayan ta ta bar gida ne wai domin na dena kwanciya da ita a lokacin hakan yasa ta fara bawa yaron mu custard da madara, Inji Abdulrazak.

Abdulrazaka ya kara da cewa duk lokacin da ya tafi zuwa ganin ta domin ya bata kudin abinci ya kan tarar da saurayin a dakinta hakan ya sa ya tabbatar Barakat makaryaciya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel