Na gwammaci shekaru 4 na Buhari a nan gaba fiye da 8 din Atiku – Shugaban UPP

Na gwammaci shekaru 4 na Buhari a nan gaba fiye da 8 din Atiku – Shugaban UPP

Shugaban jam’iyyar United Progressive Party(UPP), Cif Chekwas Okorie, ya bayyana dalilan da ya akwai bukatar ýan kudu maso gabas da ýan kudu maso yamma su mara wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya wajen ganin yayi tazarce.

A cewarsa akan zai yi saurin dawo da mulki ga mutanen yankin Kudu.

Sannan ya jaddada cewa gaskiya Najeriya bata samu abun da take bukata ba daga gwamati tun bayan yakin basasa. Ya ce lamura na dada tabarbarewa ne a kullun.

Na gwammaci shekaru 4 na Buhari a nan gaba fiye da 8 din Atiku – Shugaban UPP
Na gwammaci shekaru 4 na Buhari a nan gaba fiye da 8 din Atiku – Shugaban UPP
Asali: Depositphotos

Kan batn yaki da rashawar gwamatin Shugaban kasa Buhari ya ce tabbas gwamnatin Buhar tayi nasara akan yaki da ci hanci da rashawa, amma sai dai a cewarsa yaki da rashawa bai mutu ba a kasar.

Sannan kan batun cewa gwamnatin Buhari na bangarenci, Chekwas yace dama dole a kama wani indai ana yaki ne da rashawa, sannan kuma cewa idan har ka ga ana bibiyar mutun toh lallai yana da guntun kasha ne tsuliyar shi.

KU KARANTA KUIMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kano ta fara binciken bidiyon Ganduje

A cewarsa duk tsuntsun da ya ruwa shi ruwa ke ja. Sannan kuma ya caccaki gwamnatin PDPinda ya ce abun unya ne ma su dawo neman mulki bayn tarin barnar da suka kwashe shekaru 16 suna yi.

Ta fannin tsaro ya ce Buhari yayi kokari duk da cewar kokarinsa bai isa abunda ake bukata ba.

Ya ce ya halarci taron bikin ranar ýancin kai kuma ya ga bajintar da hukmomin saro suka yi don haka zai iya cewa ba’a taba samun ingantaccen hukumomin tsaro ba irin wannan gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel