Gwamna Ribas Wike zai marawa Atiku Abubakar baya a zaben 2019

Gwamna Ribas Wike zai marawa Atiku Abubakar baya a zaben 2019

- Gwamnan Ribas ya nuna cewa zai dage wajen ganin Atiku ya samu nasara a 2019

- Nyesom Wike dai bai goyi bayan Atiku a zaben fitar da gwani na Shugaban kasa ba

- Duk da haka Gwamnan ya nuna cewa bai da nadamar matakin da ya dauka a baya

Gwamna Ribas Wike zai marawa Atiku Abubakar baya a zaben 2019
Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike zai ba Atiku goyon baya a 2019
Asali: Twitter

Mun samu labari cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar wanda zai yi takarar Shugaban kasa a PDP ya kara samun goyon baya a Jam’iyyar adawar yayin da ake shirin zabe a farkon shekara mai zuwa.

Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya bayyana cewa zai marawa takarar Alhaji Atiku Abubakar baya a zabe mai zuwa. Gwamnan yayi wannan sanarwa ne ba da dadewa ba ta shafin sa na sadarwa na zamani watau Tuwita.

KU KARANTA: 2019: Jonathan ya nemi Inyamurai su marawa Atiku baya a PDP

Idan ba a manta ba dai Gwamnan na Ribas shi ne wanda yayi ruwa da tsaki wajen ganin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP sannan kuma ya nemi tikitin takarar Shugaban kasa.

Nyesom Wike yayi wannan dogon jawabi ne a gidan Gwamnatin Jihar Ribas da ke Garin Fatawal yace za su dafawa Atiku Abubakar wajen ganin APC ta sha kasa sannan kuma yace bai yi nadamar marawa Aminu Tambuwal baya ba.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwanwaso yayi mubaya’a ga Atiku Abubakar wanda yayi nasara a zaben tsaida ‘Dan takarar Shugaban kasa da aka yi a Jam’iyyar PDP a Jihar Ribas kwanaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel