Sau 2 Daura na zawarci na don na mara wa Buhari baya - Fayose

Sau 2 Daura na zawarci na don na mara wa Buhari baya - Fayose

Gamnan jihar Ekiti mai barin gado, Ayodele Fayose ya bayyana cewa sau biyu tsohon darakta janar na ‘yan sandan farin kaya, Lawal Daura na tuntubarsa kan ya marawa gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya, don jam’iyyar Fayose ta Peoples Democratic Party ta samu damar ci gaba da mulki a jihar.

Gwamnan wanda yi Magana a daren ranar Lahadi, 14 ga watan Oktoba a liyafar kammala mulki da takwarorinsa na kungiyar gwamnonin PDP suka shirya masa yace ya ki amincewa da bukatar sau biyu.

A wata sanarwa daga baban sakataren labaransam Mista Idowu Adelusi, a rana Litinin, 15 ga watan Oktoba yace wannan dalilin ne yasa Daura ya shirya makircin tsaro a kansa da magoya bayansa a lokacin zabe gwamna na ranar 14 ga watan Yuli a jihar.

Sau 2 Daura na zawarci na don na mara wa Buhari baya - Fayose
Sau 2 Daura na zawarci na don na mara wa Buhari baya - Fayose
Asali: Depositphotos

Fayose ya ce yayi imani da cewar Atiku Abuakar da Peter Obi za su lashe zaben shugabancin kasa na shekara mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kano ta fara binciken bidiyon Ganduje

Ya bukaci jam’iyyar da ta hade kanta don ganin sun tsige Buhari cewa ýan Najeriya na fuskantar wahala kuma sna neman PDP ta ceto su daga mulkin Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel