PDP ba zata canza Peter Obi ba – Shugaban jam’iyyar

PDP ba zata canza Peter Obi ba – Shugaban jam’iyyar

Shugaban jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, Prince Uche Secondus, ya bayyana cewa Duk da rashin amincewan manya a yankin Inyamurai, ba zata canja tsohon gwamnan jihar Anambara, Peter Obi, aa matsayin abokin tafiyan Atiku ba a zaben 2019.

Uche Secondus ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Ike Abonyi, inda ya shaidawa BBC cewa jam’iyyar ba zata maye Peter Obi da wani ma’aluki ba.

Wannan jawabi ya biyo bayan ganawar da masu ruwa da tsakin jam’iyyar PDP a yankin Kudu maso yammacin Najeriya wanda ya kunshi gwamnoni da jigogin jam’iyyar, inda suka babu wanda ta tuntubesu kafin bayyana Peter Obi a matsayin wanda zai wakilci yankin.

Ike Abonyin yace wannan abu ba zai tursasa jam’iyyar PDP canza ra’ayinta na zaban Peter Obi ba.

KU KARANTA: Gwamnan APC ya chanja shawara akan batun sauya sheka zuwa wata jam’iyya

Ya ci gaba da cewa: “Dan takarar shugabancin kasa ne da kansa yake zaben wanda zai rufa masa baya a zabe,"

"Wannan ba magana ce da gwamnonin za su fito su fada wa duniya ba, magana ce da ta kamata a yi ta a asirce."

Mun kawo muku rahoton kasar Inyamurai ba su amince da zabin da Atiku Abubakar yayi na ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa ba a karkashin Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa inda su kace sam ba a tuntube su ba.

Osita Chidoka da wasu Jiga-jigai a Kasar Inyamurai ba su yi na’am da da Peter Obi a matsayin ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa ba inda su ke ganin wasu ne dabam su ka cancanta ba shi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel