Wata mata ta fado ta mutu daga saman bene na 27 yayinda take kokarin daukar hoton selfie (hotuna)

Wata mata ta fado ta mutu daga saman bene na 27 yayinda take kokarin daukar hoton selfie (hotuna)

Daukar hotunan tarihi na da matukar muhimmanci, sannan mutane kan yi duk wani abu da suka ga za su iya domin daukar kyawawan hotunan kansu don su yada a shafukan zumunta a kokarinsu na ganin sun burge abokansu da dai sauransu.

Sai dai ga wasu mutane, a kokarinsu na ganin sun dauki kyawawan hotuna sai su hadu da ajalinsu ba tare da sun shirya ba.

Bisa ga rahoto, daukar hoton da ake ma lakabi da selfie yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 250 tun 2011, sannan kuma babu alamu da ke nuna cewa mutane za su bar wannan tsari na daukar hoton na kusa.

Legit.ng ta tattaro cewa wata mata mai shekaru 27 a duniya a Panama mai suna Sandra Manuela Da Costa Macedo, ta fado ta mutu daga ginin bene na hawa 27 yayinda take kokarin daukar selfie.

KU KARANTA KUMA: Na saci babur ne don kula da jin dadin budurwata – Mai laifi

Matar wacce da yara biyu a duniya na zaune a harabar benan lokacin da ta juya baya sannan ta fadi.

An tattaro cewa iska mai karfi ne yayi sanadiyar hankada tat a baya har ta fadi.

Wata mata ta fado ta mutu daga saman bene na 27 yayinda take kokarin daukar hoton selfie (hotuna)
Wata mata ta fado ta mutu daga saman bene na 27 yayinda take kokarin daukar hoton selfie
Asali: Instagram

Rahotanni sun nuna cewa Sandra malamar makaranta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel