Jerin sunayen wasu mutane 50 da aka haramtawa fita daga Najeriya: Ba mu san zancen ba - Fadar Shugaban Kasa

Jerin sunayen wasu mutane 50 da aka haramtawa fita daga Najeriya: Ba mu san zancen ba - Fadar Shugaban Kasa

- Fadar shugaban kasa ta nesanta kanta daga jerin sunayen mutane 50 da aka haramtawa fita kasashen waje

- Fadar shugaban kasar ta ce ba ta fitar da sunan kowa ba kuma ba za ta fitar da sunayen a nan gaba ba

Fadar shugaban kasa ta nesanta kanta daga jerin sunayen mutane 50 da aka haramtawa fita kasashen waje bisa zarginsu da mallakar dukiya ta haramtaciyar hanya.

A ranar Asabar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da kafa wata dokar haramtawa wasu manyan mutane 50 fita kasashen waje saboda zargin rashawa. An kafa dokar ne bayan shugaba Buhari ya saka hannu kan Executive Order 6.

Jerin sunayen wasu mutane 50 da aka haramtawa fita daga Najeriya: Ba mu san zancen ba - Fadar Shugaban Kasa
Jerin sunayen wasu mutane 50 da aka haramtawa fita daga Najeriya: Ba mu san zancen ba - Fadar Shugaban Kasa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Siyasar Kano: Takai ya karbo tutar takara daga Abuja (Hotuna)

Jim kadan bayan sanar da kafa dokar wasu kafafen yada labarai sun fara wallafa sunayen wasu mutane da ke cikin jerin wanda aka haramtawa fita kasashen wajen.

Sai dai babban mai taimakawa shugaban kasa a fanin kafafen yada labarai, Malam Garba Shehu ya ce fadar shugaban kasa ba ta fitar da sunayen ba kuma ba za ta bayyana sunayen mutanen da dokar ya shafa ba.

"Kan batun sunayen wadanda aka haramtawa fita kasahen waje, ina son in tabbatar da cewar ba mu fitar da jerin sunaye ba kuma ba zamu bayyana sunayensu ba," inji Shehu.

Mutane da dama musamman 'yan jam'iyyar hamayya sunyi tir da wannan dokar inda suka kamanta da da mulkin kama karya da daniyya, inda su kayi kira da al'umma masu kishin demokradiyya su tashi tsaye domin yakar dokar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel