Gwamnan APC ya chanja shawara akan batun sauya sheka zuwa wata jam’iyya

Gwamnan APC ya chanja shawara akan batun sauya sheka zuwa wata jam’iyya

- Gwamna Ibikunle Amosun ya chanja shawarar barin jam'iyyar APC

- Ya sauko daga dokin naki da ya hau akan dan takarar gwamnan jam'iyyar a jihar

- Hakan ya samo asali ne sakamakon tausar sa da shugabannin jam'iyyar na jihar suka yi

Sabanin yadda wasu da dama ke ta zaton cewa Gwamna Ibinkunle Amosun na jihar Ogun zai sanar da batun sauya shekar sa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jiya, alamu masu karfi sun nuna cewa gwamnan ya chanja shawarar sauya shekar nasa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wasu shugabannin jam’iyyar a jihar sun taushi Amosun da sauya shewara akan shirinsa na barin APC zuwa wata jam’iyya yayinda yake zanga-zanga akan billowar wani mai sana’ar mai Dapo Abiodun a matsayin dan takarar gwamna a jihar.

Gwamnan APC ya chanja shawara akan batun sauya sheka zuwa wata jam’iyya
Gwamnan APC ya chanja shawara akan batun sauya sheka zuwa wata jam’iyya
Asali: UGC

An ruwaito cewa Amosun chanja shawarar sauya sheka saboda kin amincewar masu masa biyayya wajen bin sa zuwa wata jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: 2019: Gwamnan Kano ya kafa wani kwamitin sulhu a Jam’iyyar APC

A halin da ake ciki, magoya bayan APC a fadin kananan hukumomi 20 na jihar sun kai ziyarar ban girma gad an takarar gwamna Dapo Abiodun a gidansa dake yankin Iperu na mazabar Ogun ta gabas.

Da yake jawabi a taron, darakta janar nay akin neman zaben Gwamna Ibikunle Amosun a zaben 2015, Cif Bode Mustapha ya bukaci fusatattun yan jam’iyya da su hada hannu wajen ganin dan takarar jam’iyyar yayi nasara a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel