2019: Gwamnan Kano ya kafa wani kwamitin sulhu a Jam’iyyar APC

2019: Gwamnan Kano ya kafa wani kwamitin sulhu a Jam’iyyar APC

– Gwamna Abdullahi Ganduje ya nada kwamiti domin duba rikicin APC

– Rigima ta barke a cikin APC tun bayan zaben fitar da gwani da aka yi

– Kwamitin mai mutum 12 za su shawo karshen rikicin cikin gidan na APC

2019: Gwamnan Kano ya kafa wani kwamitin sulhu a Jam’iyyar APC
Wani kwamiti zai duba rikicin Jam'iyyar APC a Jihar Kano
Asali: Facebook

Mun samu labari cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya kaddamar da wani kwamitin mutane 12 da za su duba rikicin da ya barke a Jam’iyyar APC a sakamkon zaben fitar da gwani da aka yi a Jihar Kano a kwanakin baya.

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi wai zama jiya a cikin gidan Gwamnati inda ya kaddamar da kwamitin da zai duba sabanin da aka samu a APC wajen tsaida ‘Yan takaran Jihar Kano.

KU KARANTA: Bidiyon cin hanci: Daily Nigerian ta shirya zuwa Kotu da Gwamnan Kano

Abba Anwar ya bayyanawa ‘Yan jarida wannan a Ranar Lahadi. A jawabin dai Gwamnan ya nuna cewa siyasa ta gaji sabani. Wannan dai na zuwa ne lokacin da ake zargin Gwamnan da karbar cin hanci wajen’Yan kwangila.

Janar Bashir Magashi mai ritaya shi ne wanda zai jagoranci wannan kwamiti. Sauran ‘Yan kwamitin sun hada da Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano Kabiru Rurum da tsohon Kakakin Jihar Yusuf Ata da kuma Alhaji Kabiru Rabiu.

A cikin kwamitin akwai irin su Janar Jafaru Isah, Sheikh Ibrahim Khalil, Barista da Garba Yusuf Abubakar. Har wa yau, kwamitin ya kunshi mutane irin su Amadu Haruna Zago da kuma Musa Salihu Riruwai a matsayin Sakataren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel