Peter Obi: Goodluck Jonathan yana nemawa Atiku Abubakar goyon bayan Inyamurai

Peter Obi: Goodluck Jonathan yana nemawa Atiku Abubakar goyon bayan Inyamurai

- Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nemi ‘Yan kudu su marawa Atiku baya

- Jonathan yayi kira ga Inyamurai su amince da zabin d Atiku yayi na daukar Peter Obi

- Jonathan ya fadawa Inyamurai su guji matsawa Atiku lamba game da Abokin takara

Peter Obi: Goodluck Jonathan yana nemawa Atiku Abubakar goyon bayan Inyamurai
Jonathan yace ya kamata a girmama zabin da Atiku yayi a PDP
Asali: UGC

Dazu mu ka samu labari cewa tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya nemi Inyamurai su marawa Atiku Abubakar da Abokin takaran sa da ya dauka watau Peter Obi baya a Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa na 2019.

Tsohon Shugaban na Najeriya ya nemi Manyan Kasar Inyamurai su daina korafe-korafe su yi na’am da zabin da Atiku yayi na dauko tsohon Gwamna Peter Obi a matsayin ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa a 2019.

KU KARANTA: 2019: Manyan Kasar Ibo sun nuna tsagoron adawar su ga Peter Obi

A wani dogon jawabi, Dr. Jonathan ya fadawa Manyan na Kasar Kudu su guji kai Atiku bango a kan Abokin takaran sa. Wasu manya da ake ji da su a Kasar Inyamurai dai sun nuna cewa Atiku bai tuntube su kafin ya dauki Peter Obi ba.

Yanzu dai wasu Dattawa a Yankin Kudu-maso-Gabashin Kasar sun fito sun nuna adawar su da takarar Peter Obi wanda su ka ganin bai dace da Mataimakin Shugaban kasa ba. Jonathan yace ya kamata ajiye duk banbanci ayi wa PDP aiki.

Jonathan ya taya duk wanda su ka samu nasarar wajen karbar tikiti a Jam’iyyar PDP murna inda ya nemi Jam’iyyar tadage wajen kai ga nasara a 2019. Wasu dai a Kasar Inyamurai su na ganin Peter Obi bai da farin jinin da zai ci zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel