Shan koko kwanciyar rai: Matasa 5 sun kama hanyar Adamawa a kasa don soyayyar Atiku

Shan koko kwanciyar rai: Matasa 5 sun kama hanyar Adamawa a kasa don soyayyar Atiku

A yanzu haka wata gungun matasa su biyar ta kama hanyar jahar Adamawa a kasa tun daga jahar Bauchi don bayyana kaunarsu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Larabar da ta gabata ne wadannan matasa suka tashi daga Bauchi, da misalin karfe 12 na rana, inda suka bayyana dalilin wannan tattaki nasu da cewa soyayyar Atiku ce da bayyana goyon bayansu a gareshi musamman bisa burinsa na zama shugaban kasa.

KU KARANTA: Yan sanda sun gayyaci dan takarar gwamnan Kano na PDP kan kisan tsoho dan shekara 70

Jagoran matafiyan, Hassan Mahmud ya kara da cewa suna yi wannan tattaki ne don ganin an samu shugaban kasar Najeriya daga yankin Arewa naso gabashin kasarnan, domin a cewarsu ba ayi da su.

Shan koko kwanciyar rai: Matasa uku sun kama hanyar Adamawa a kasa don soyayyar Atiku
Matasan
Asali: Facebook

“Za’a samu cigaba sosai Idan shiyyar Arewa maso gabas ta samu shugaban kasa, musamman shawo kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye yankin, bugu da kari idan ba dan shiyyar ba, babu wanda zai iya kawar da wannan matsala.” Inji shi.

Da yake jawabi akan yadda suka shirya wannan tattaki, Hassan yace shine ya tsara wannan tafiyar, kuma yayi haka ne domin janyo hankulan jama’a game da wariyar da ake nuna ma yankin Arewa gabas, inda yace tun baya dawowar Najeriya bisa turbar Dimukradiyya, ba a taba samun shugaban kasa daga yankin Arewa maso gabas ba.

Bugu da kari jagoran matafiyan ya cigaba da cewa suna dane da irin kalubalen da cikin wannan tafiya, don haka a shirya suke ta isashshen guzurin da zai ishesu har su isa Adamawa, kuma yace sun sanar da hukumomin tsaro game da tafiyar tasu.

Daga karshe yace yana sa ran a cikin kwanaki hudu zasu isa jahar Adamawa, amma idan kuma an samu akasi toh lallai babu gudu babu ka da baya sai sun isa jahar Adamawa a kasa. Sai dai yace zasu tsaya a Gombe don jajanta ma gwamna Dankwambo bisa kayen da ya sha.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel