An kama ja'iri yana lalata da mata kanana a tare, N50-N50 kuwa ya basu shegen

An kama ja'iri yana lalata da mata kanana a tare, N50-N50 kuwa ya basu shegen

- Yan sanda sun kama wani Dan kasar Togo da laifin lalata da kananan yara

- Naira hamsin hamsin yake basu domin lalata dasu

- An kama shi ne bayan korafin da mahaifin daya daga cikin yaran ya kaiwa yan sanda

An kama ja'iri yana lalata da mata kanana a tare, N50-N50 kuwa ya basu shegen
An kama ja'iri yana lalata da mata kanana a tare, N50-N50 kuwa ya basu shegen
Asali: Facebook

Yansanda sun damke wani Dan kasar Togo da laifin lalata da kananan yammata.

Naira hamsin hamsin yake basu a duk lokacin da zaiyi lalata dasu.

Hukumar yan sandan Ejigbo ne suka kama Dominic Samson mai shekaru 31 a duniya a ranar litinin bayan da mahaifin daya daga cikin yammatan mai shekaru 15 ya kawo kara.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan, CSP Chike Oti, yace makwafta ne suka kama Samson na lalata da yarinyar mai shekaru 15 a lamba 28 titin Olusesan, Ejigbo.

Makwaftan sun sanar da mahaifin yarinya wanda ya tafi wurin aiki. Daga baya ne yazo ya sanar da hukumar yan sandan.

Oti yace : Bayan kawo karar, DPO wacce mace ce tayi wa yarinyar tambayoyi kuma ta tabbatar da rahoton.

"Ta tabbatar da cewa ba wai lalata kadai yake da yarinyar ba, har ta dubura yake saduwa da ita."

"Yarinyar ta bayyana ba da ita kadai yake lalata ba. Har da wasu yara biyar masu shekaru tsakani 13 zuwa 15."

DUBA WANNAN: Jirgin kasa daga Warri ya iso Arewa

"An kawo sauran yaran inda akayi musu tambayoyi kuma suka tabbatar da hakan. Yammatan sunce wanda ake zargin na basu Naira hamsin hamsin ne bayan ya gama lalata dasu."

Kamar yanda yace, an kai yaran asibiti inda rahoton likita ya nuna duk an lalata su.

Kwamishinan yan sandan, Imohimi Edgal, ya shawarci iyaye da su dinga kula da yaransu domin wannan ne kadai mafita.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel