An kammala aikin jirgin kasa daga Warri har Arewa a makon nan

An kammala aikin jirgin kasa daga Warri har Arewa a makon nan

- Gwamnatin tarayya ta bayyana kammala titin jirgin kasa daga Warri zuwa Itakpe

- Kammalar aikin zai bude hanyoyin kasuwanci ga yankin

- Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin samar da sababbin hanyoyin samar da arziki ta hanyar habaka ma'adanan kasar

Majalisar dinkin duniya tace kusan mutum miliyan daya ne basu samun agaji a Najeriya
Majalisar dinkin duniya tace kusan mutum miliyan daya ne basu samun agaji a Najeriya
Asali: Twitter

Gwamnatin tarayya ta bayyana kammala titin jirgin da ya fara daga filin jirgin ruwa na Warri, ya ratsa zuwa Ajaokuta zuwa Itakpe.

Karamin ministan habaka ma'adanai da karafa, Hon Abubakar Bwari yace kammala titin jirgin kasan zai samar da sauki gurin tsallake teku da kuma bude sababbin damammaki ga kamfanonin karafa na Ajaokuta da Delta.

Ya kara da cewa kammala fadada rafin Niger da kuma hanyoyin ruwan Warri zai kara karfin shige da ficen kaya zuwa kasashen ketare ta ruwan Warri.

DUBA WANNAN: Yanzunnan Shugaba @MBuhari ya rattaba hannu kan dokar takunkumi kan mutum 50 daga manyan kasar nan

Bwari ya bayyana cewa ma'aikatar su ta karfafa dokoki ga masu saka hannun jari a bangaren ma'adanai domin saukaka harkar hakar ma'adanai a Najeriya.

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin samar da sababbin hanyoyin samar da arziki ta hanyar habaka ma'adanan kasar.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel