Aljannu dubunnai sun amshi darikar Tijjaniyya daga hannun Sheikh Dahiru Bauchi, inji rahotanni

Aljannu dubunnai sun amshi darikar Tijjaniyya daga hannun Sheikh Dahiru Bauchi, inji rahotanni

- Ana yawan danganta malamai da Shaihunnai da iya magana da Aljannu

- Kimiyya ta tabbatar babu Aljannu, tace duk tsatsuniya ce

- Ana yin rukiyya a addinan Hindu, Islama da ma na Masihiyya

Aljannu dubunnai sun amshi darikar Kadiriyya daga hannun Sheikh Dahiru Bauchi, inji rahotanni
Aljannu dubunnai sun amshi darikar Kadiriyya daga hannun Sheikh Dahiru Bauchi, inji rahotanni
Asali: Twitter

Rahotanni a shafukan sada zumunta dake yawo, wadanda muka samo muku, na bayyana yadda wani babban malami wai ya shigar da dubban aljannu cikin mazhabarsa ta darika a Najeriya.

A rahoton da jaridar Inside Arewar ta wallafa, ya nuna cewa, aljannun sun karbi darikar da Sheikh Dahiru Bauchi ke wa hidima ne watau Tijjaniyya.

Aljannu dubunnai sun amshi darikar Tijjaniyya daga hannun Sheikh Dahiru Bauchi, inji rahotanni
Aljannu dubunnai sun amshi darikar Tijjaniyya daga hannun Sheikh Dahiru Bauchi, inji rahotanni
Asali: Twitter

A Najeriya dai akwai miliyoyin mutane dake bin wannan darika, musamman a cikin wadanda basu da karancin ilimin zamani na Boko.

DUBA WANNAN: Man fetur ya dan farfado a duniya

An sha jin karamar irin wadannan Shaihunnai, inda akan je don daukar karatu ko tubarraki wurinsu.

Tarihihi ya nuna yadda a baya ma ake cewa wai Usmanu DanFodio ya musuluntar da Aljannu da dama, kuma yana basu karatu a bisa saman tsaunuka a zamaninsa.

Babu dai wata hujja da ta nuna akwai aljannu a zahiri, sai dai canki-canka ta addinai da tatsuniyoyin mutanen da.

Ana yin rukiyyar cire aljannu a addinin Hindu, Islama, da Kiristanci, amma kasashe masu ilimi baka taba samunsu da matsalar aljannu, wannan ya sa baka jin ana karantar da aikin aljanu ko maganinsu a ajin Biology ko na Medicine.

A bara war haka ma, ance Shaihun Malamin ya musuluntar da wani katoton bakin aljani, sai dai kamar mutane na yawan danganta bakar fata kenan da mugunta ko kafirci, farar fata kuma da kirki.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel