Hanyoyi 6 da ake amfani da goro da ya dace ku sani

Hanyoyi 6 da ake amfani da goro da ya dace ku sani

Goro dai yana da matukar muhimmanci ga al'ummar Najeriya na Kudu, Arewa da Yamma kuma yawancin mutane sun ana amfani da goron wajen magance wasu mataloli na lafiya.

Sai dai baya ga amfani da goron wajen yin magani, ko kun san cewa akwai hanyoyi da yawa da al'umma ke amfani da goro domin biyan wasu bukatu na yau da kulum.

Ku biyo mu a hankali domin sanin wasu daga cikin hanyoyin da ake iya amfani da goro a harkokin yau da kulum.

Wasu hanyoyi 10 da ake amfani da goro da ya dace ku sani
Wasu hanyoyi 10 da ake amfani da goro da ya dace ku sani
Asali: UGC

Hanyoyin da ake amfani da goro

1. Ana amfani da goro a matsayin kudi

A shekaru masu yawa da suka gabata, al'umma a kasashen yammacin Afirka suna amfani da goro a matsayin kudi, misali shine mutanen Senegal da Mali kuma har yanzu akwai wadanda ke amfani da goro wajen musayar kasuwanci.

Duk da yake cewar galibin mutane sun dena amfani da goro a matsayin kudi, har yanzu ana amfani da shi wajen cikinikin sadaki musamman da wasu harkokin musamman a kudu.

2. Ana amfani da goro wajen bukukuwan addini

Al'ummar yankin Afirka ta Yamma sun dade suna amfani da goro wajen gudanar da wasu ababen da suka shafi addini na gargajiya musamman kabilar igbo da Yarabawa.

Suna amfani da goro wajen magana da dodaninsu da kuma magabata da suka mutu shekaru da dama sannan ana amfani da goro wajen wasu addu'o'i da tarbar baki.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Kotu za ta janye belin da ta bawa tsohon gwamnan PDP

3. Ana amfani da goro wajen magance maye

Duk da cewa masana ba su gudanar da sahihiyar bincike kan wannan lamarin ba, mutane da dama suna amfani da goro domin maganin maye ta giya ko wasu ababen da ke janyo maye.

4. Karin kuzari

Shin ko ka lura cewar duk lokacin da ci goro kana kara samun kuzari? Hakan na faruwa ne saboda goro yana dauke da sinadarin caffeine wanda ke kara kuzari.

An fara amfani da goro (Kola) wajen samar da kuzari duk lokacin yakin duniya na farko inda sojoji ke amfani dashi domin kada suyi barci. Wasu direbobin mota ma na amfani da goro domin kawar da barci.

5. Rage kiba

Idan kana son ka rage kiba, toh ka jibinci cin goro domin idan ka ci goro, za ka lura cewar ba ka jin yunwa sosai sai dai ka rika shan ruwa.

An kuma bayyana cewar goro ya kan inganta yadda jikin mutum ke sarrafa abinci da fitar da abinda bashi da amfani daga jiki.

6. Maganin ciwon kai

Goro na dauke da sinadarin caffeine da theobromine hakan yasa ya ke magance ciwon kai. Sai dai idan mutum ya kura cewar ciwon kan nasa ya tsananta, zai ya garzaya wajen likita a duba shi saboda daukan mataki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel