Madalla: Aikin ginin sabuwar matatar man fetur ya kankama a Najeriya

Madalla: Aikin ginin sabuwar matatar man fetur ya kankama a Najeriya

Wani kamfani na kwararrun 'yan kasuwa na Waltersmith Refining and Petrochemical Company Limited a turance ya bayyana kudurin sa na aiki gadab-gadan wajen kamma gina matatar man fetur mai girman gaske da ka iya tace litar danyen mai miliyan 271 a shekara a Najeriya.

Madalla: Aikin ginin sabuwar matatar man fetur ya kankama a Najeriya
Madalla: Aikin ginin sabuwar matatar man fetur ya kankama a Najeriya
Asali: Depositphotos

Shugaban kamfanin, Mista Abdulrazaq Isa shine ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa inda ya bayyana cewa matar man za ta taimaka matuka wajen kara habaka tattalin arzikin kasar Najeriya.

Legit.ng haka zalika mun samu cewa Mista Abdurrazaq Isa ya ce a garin Ibigwe ne dake a karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo ne za su gina matatar man.

Ya kara da cewa matatar man idan har suka kammala ta zata rika tace gangar danyen man 5,000 kafin daga bisani su kara inganta ta ta wuce hakan nan gaba kadan.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari a jiya ya roki malaman addinai a Najeriya da su taimaka ma gwamnatin sa wajen ganin ta yi nasa a yakin da take yi da 'yan ta'addan dake boyewa cikin rigar addini.

Shugaban kasar yayi wannan roko ne a lokacin da ya karbin bakuncin shugabannin kungiyar Qdiriyya ta Afrika a karkashin jagorancin shugaban ta Sheikh Qribullah Nasiru Kabara a fadar sa dake a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel